Yadda Cutar Kansa Ta Sauya Wani Matashi Mai Jini A Jika, Hotunansa Za Su Tsuma Zuciyar Kowaye

Yadda Cutar Kansa Ta Sauya Wani Matashi Mai Jini A Jika, Hotunansa Za Su Tsuma Zuciyar Kowaye

  • Allah ya jarabci matashin Hashim Raza da rashin lafiya ta cutar kansar ciki da kayan ciki wanda ya kai mataki na hudu
  • Komai ya sauya a rayuwar Raza domin hatta ga kamanninsa sun sauya kamar ba shi ba, sannan ana nema masa taimako
  • Zafin ciwo bai sa bawan Allan yanke kauna daga rahamar Ubangiji ba duk da ya ce bai san mai gaba za ta yi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani matashi mai suna Hashim Raza ya hadu da ibtila’i na rashin lafiya wanda ya kai har halittan jikinsa sun sauya.

Likitoci dai sun gano cewa Raza na dauke da cutar kansar ciki da na kayan ciki wanda har sun kai mataki na '4', shafin Convert to Islam ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Hashim Raza
Hashim Raza: Yadda Cutar Kansa Ta Sauya Wani Matashi Jini A Jika, Hotunansa Za Su Tsuma Zuciyar Kowaye Hoto: Converts to Islam
Asali: Facebook

Kamar yadda shi kansa matashin ya bayyana a shafinsa na Facebook, ya ce an yi masa tiyaa a cikinsa a ranar 5 ga watan Yunin 2021.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Sai dai kuma wani abun birgewa da shi shine bai karaya ba duk da wannan ibtila’I da Allah ya jarabce shi da shi domin ya ce ya yarda da duk wani hukunci da Allah ya zartar a kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafinsa:

“A shekarar da ta gabata an yi mani tiyasa a ranar 5 ga watan Yuni kuma nay i bikin zagayowar ranar haihuwata a asibiti. Shekara daya ta wuce kuma wannan shekara dayar ta sauya rayuwata gaba daya.”
“Ban san me gaba ya tanada ba a gare ni kuma ko zan tashi daga wannan rashin lafiya ko ba zan tashi ba amma na yarda da duk wasu tanade-tanade da Allah ya yi mun.”

Hakazalika mujallar People Magazine Pakitan ya je shafinsa na don nemawa matashin tallafi da taimako inda ta nemi mutane da su taimaka masa wajen nasara kan wannan cuta da ta addabe shi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashi mai shekaru 18 ya kera mota daga tarkacen karfe, ya ba da mamaki

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara Mai Yara 18

A wani labari na daban, magidancin nan mai mata uku da yara 18 wadanda hotunansu suka yi fice a shafukan soshiyal midiya a lokacin bikin babban Sallah, Mohammed Suleiman ya magantu a kan iyalin nasa.

Mallam Sulaiman wanda ya kasance lakcara a kwalejin ilimi na Umar Bn Khattab da ke Kaduna ya bayyana cewa ko kadan baya wasa da jin dadin iyalinsa duk da yawan da suke da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng