An samu tsaiko yayin da 'yan zanga-zangar NLC suka mamaye mashigar sakateriyar tarayya

An samu tsaiko yayin da 'yan zanga-zangar NLC suka mamaye mashigar sakateriyar tarayya

Gangamin hadin gwiwa da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta gudanar ya haifar da cikas a manyan titunan da ke kan hanyar zuwa sakatariyar gwamnatin tarayya, Abuja.

Kungiyar na gudanar da wani gagarumin gangami domin nuna goyon baya ga kungiyoyin malaman jami’o’in (ASUU) da ke yajin aiki tun watan Fabrairu, 2022, The Nation ta ruwaito.

NLC ta mamaye sakateriyar tarayya
Tashin hankali yayin da 'yan zanga-zangar NLC suka mamaye sakateriyar tarayya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Da yake jawabi ga ma’aikatan a shiyya ta uku da ke Abuja, Shugaban Kungiyar ASUU, Kwamared Ibrahim Mohammed ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya bukatun kungiyoyin.

Mohammed ya lura cewa tsarin jami'o'in ba zai iya ci gaba da yadda gwamnati ke tafiyar da lamurra ba.

Ma'aikatan na kan wannan gangamin hadin kai har zuwa majalisar dokokin kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.