Daniel Okoh Shine Sabon Shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya CAN

Daniel Okoh Shine Sabon Shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya CAN

  • An zabi Babban Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN
  • Wa’adin shugaban Kungiyar CAN mai Martaba Samson Olusupo-Ayokunle da sauran shugabannin zartarwa na kasa dake cikin tawagarsa ya zo karshe
  • Shugaban CAN mai barin gado ya godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da addu’o’in da suke mi shi

Abuja - An zabi Babban Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN. Rahoton The Guardian

Sanarwar hakan na kunshe ne a wata jawabi da babban sakataren kungiyar ta CAN, Mista Joseph Daramola ya fitar jiya a Abuja.

Okoh shine Babban Shugaban Cocin Christ Holy Church, wanda kuma ake kira Nation Builders (Odozi-Obodo).

CAN ta ƙunshi ƙungiyoyi biyar wanda ya hada da Majalisar Kirista ta Najeriya (CCN), Sakatariyar Katolika ta Najeriya (CSN), Fellowship Christian Pentecostal of Nigeria (CPFN)/Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), Ƙungiyar Ikklisiya ta Afirka (OAIC), TEKAN da ECWA Fellowship.

Kara karanta wannan

Lauya ya Kai Tinubu Gaban Kotu, Ana Neman Hana Sa Takara Saboda Dauko Musulmi

Okoni
Daniel Okoh Shine Sabon Shugaban Kungiyar Kristocin NajeriyaCAN The Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar kiristocin Najeriya ta shirya gudanar da babban taronta a ranar 27 ga watan Yuli, wanda zai kafa sabuwar gwamnati.

Majalisar ta kuma kawo karshen wa’adin Mai Martaba Samson Olusupo-Ayokunle da sauran shugabannin zartarwa na kasa a cikin tawagarsa.

Shugaban CAN mai barin gado ya godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi da kuma addu’o’in da suka mi shi, wanda ya sa ya samu nasarar gudanar da aikinsa.

"Gumi Na Ne", Faston Da Aka Yi Wa Fashin Gwala-Gwalai Yayin Da Ya Ke Wa'azi A Mimbari A Coci Ya Magantu

A wani labari kuma, Limamin coci 'dan kwalisa' na jihar Brooklyn wanda ya saba nuna kayayyakinsa masu tsada ya kare kansa bisa rayuwa ta tunkaho da ya ke yi bayan an masa fashi yana tsakar wa'azi, rahoton Lindaikeji.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya Bada Sabon Mukami, ya Maye Gurbin Wanda ya ba Minista a Kano

Bishop Lamor Miller-Whitehead wanda ke kan mimbari lokacin da wasu mutane suka shigo cocin suka sace masa kayan allatu tare da na matarsa da kudinsu ya kai $1m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa