Wani Matashi ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa har Lahira kan rikicin Fili a Nasarawa

Wani Matashi ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa har Lahira kan rikicin Fili a Nasarawa

  • Wani mai suna Tunde Badejo ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa har lahira kan wani saɓani da ya shiga tsakanin su a Nasarawa
  • Matar Mamacin ta ce tun shekara ɗaya da ta gabata ɗan ya addabi mahaifinsa ya yankar masa wani fili da yake mallakin iyalai baki ɗaya
  • A halin yanzun ɗan mamacin na biyu ya ce sun kai wa yan sanda rahoto kuma sun kai gawar ɗakin aje gawarwaki

Nasarawa - Mazauna garin Masaka a ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa sun shiga cikin ruɗani da tashin hankali bayan wani mutumi ya rasa rayuwarsa a hannun ɗansa na fari.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗan mai suna Tunde Badejo, ya daba wa mahaifinsa Badejo Idowu, wuƙa ba sau ɗaya ba har ya mutu kan mallakar gona wacce yake ta iyalan gidan ce.

Kara karanta wannan

'Ina tausaya wa sauran' Fasinjan Jirgin ƙasan Kaduna da ya kubuta ya magantu kan Bidiyon dukan Fasinjoji

Taswirar jihar Nasarawa.
Wani Matashi ya ɗaɓa wa mahaifinsa wuƙa har Lahira kan rikicin Fili a Nasarawa Hoto: punchng
Asali: UGC

City & Crime ta tattaro cewa Tunde ya addabi mahaifin na sa kan ya mallaka mishi wani yankin ƙasar gonan tun sama da shekara ɗaya nan baya.

Matar mamacin, Madam Tolani Badejo, ta shaida wa wakilin jaridar yayin da ya ziyarci wurin da abun ya faru cewa mijinta ya amince kuma ya roki Tunde ya ba shi lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bayananta, Matar mamacin ta bayyana cewa mijinta ya nemi lokacin ne domin a raba filin gonar ga kowane mamban iyalan gidan cikin adalci ba tare da tauye haƙƙi ba.

Madam Tolani ta ce:

"Tun shekarar da ta gabata ya damu Mijina kan batun gonar, to a lokacin da suka samu saɓani na ƙarshe ranar Litinin, sai ya zare wuƙa ya daɓa wa mahaifinsa a wurare da dama."
"Ya daɓa masa wuka a kai, wuya, ƙirji, hannuwa da ƙafafu har rai ya yi halinsa. Na nemi ɗauki amma ya tsere."

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Gwamnan PDP ya maida wa Atiku martani kan kalamansa na zaɓen mataimaki

Wane mataki aka ɗauka?

Ɗa na biyu ga mamacin, Ayomide Badejo, ya ce tuni suka kai rahoton abun da ya faru ga yan sanda yayin da aka kai gawar mahaifin su ɗakin aje gawarwaki.

A wani labarin kuma An bayyana sunaye da bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe a Abuja

A jiya Litinin ne wasu yan ta'adda suka mamayi dakarun soji da ke tsaron fadar shugaban ƙasa a yankin Bwari a Abuja.

Harin ya yi sanadin mutuwar jami'ai guda uku, cikakken bayanan wasu daga cikin mamatan sun bayyana mun tattara muku su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262