Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Huɗu, Sun Sace Wasu 30 a Sabon Harin Zamfara

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Huɗu, Sun Sace Wasu 30 a Sabon Harin Zamfara

  • Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Morai, ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamafara, inda suka kashe mutum huɗu
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun sace aƙalla mutum 30 a harin wanda ya kasance na farko a kauyen
  • Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen Zamfara ya ce zai bincika ainihin abinda ya faru kamin ya yi tsokaci

Zamfara - Mazauna sun bayyana cewa mutum hudu sun rasa rayuwarsu yayin da aka sace wasu 30 lokacin da yan bindiga suka shiga ƙauyen Morai da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara, a jihar Zamfara da safiyar Litinin.

Premium Times ta rahoto mazauna ƙauyen na cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 02:30 na dare, suka yi ta aikata nufin su har karfe 6:15 na Asubahi.

Harin yan bindiga a Zamfara.
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Huɗu, Sun Sace Wasu 30 a Sabon Harin Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen, Mansur Zainu, ya ce wannan shi ne karo na farko da yan bindiga suka kai hari garin, kuma shi ne na biyu mafi girma a yankin ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jihar arewa, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata

"Sun kai hari ƙauyukan da ke zagaye da mu amma karo na farko kenan suka shigo mana kuma lamarin ya yi muni. Yan Bijilanti sun yi kokarin korar su amma sanin kowa ne sun fi su manyan makamai." inji Mansur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutum nawa harin ya shafa?

A cewar Mista Zainu, yan bindigan sun kashe mutum uku da wani ƙaramin yaro ɗaya cikin su har da Sarkin Fawan garin, Sani Na'ayi da Yahaya Muhammad, wani ɗan kasuwa.

Zainu ya ce:

"Bamu san ta yadda aka kashe su ba saboda sai bayan harin muka gano gawarsu lokacin da muka dawo cikin gari amma zata iya yuwuwa harbe su aka yi a kokarin guduwa kamar sauran mutane."

Ƙanin wanda aka kashe, Yahaya Muhammed, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce matar mamacin, kawunsa da surukarsa suna cikin waɗan da maharan suka sace.

Kara karanta wannan

Dubun wasu Sojojin bogi huɗu ya cika, An cafke su da tsakar dare

"Lokacin da yan bindigan suka shigo, Yahaya ne na farko da ya gudu bisa rashin sa'a sai ya faɗi, ba zai iya gudu sosai ba, sai ya ɓuya a bayan wani wuri. Wani ɗan bindiga ya hango shi, ya je ya harbe shi sau biyu a kai," a cewar mutumin.

Shin jami'an tsaro sun samu rahoto?

Da aka tuntuɓe shi, kakakin hukumar yan sandan Zamfara, Muhammad Shehu, ya nemi a ba shi awa ɗaya ya bincika ainihin abun da ya faru kafin ya yi tsokaci.

Bayan awanni biyu aka sake neman sa amma bai ɗaga kiran ba kuma bai dawo amsar sakonnin da aka tura masa ba.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jiha, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata

Tashin hankali da tsoro ya mamaye zuƙatan mazauna Jalingo, babban birnin jihar Taraba yayin da ƙarar harbe-harbe ya karaɗe birnin lokacin da yan bindiga suka kai hari da tsakar daren Litinin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya a Katsina, sun kashe rayuka

'Yan bindigan, a rahoton da Daily Trust ta tattara, sun kashe mutum uku kuma suka yi awon gaba da shugaban dakarun tsaron Bijilanti na garin da wasu ƴan mata biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262