Bidiyon budurwa mai shekaru 23 da tayi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89

Bidiyon budurwa mai shekaru 23 da tayi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89

  • Wata matashiyar zukekiyar budurwa ta janyo mahawara a dandalin sada zumuntar zamani bayan ta aure mahaifin saurayinta
  • Budurwar mai shekaru 23 ta dauka wannan matakin ne bayan ta kama saurayin nata da mata daban-daban yana cin amanarta
  • Bayan tayi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89, alakarta da saurayin ta koma ta tsohon saurayi da kishiyar maman shi

Wata mtashiyar budurwa ta aure mahaifin saurayinta mai shekaru 89 bayan ta kama saurayin nata yana cin amanarta

Wani hoton budurwar mai shekaru 23 tare da tsohon mijinta ya yadu a Instagram bayan shafi mai suna The Savoy Show ya wallafa.

Tayi Wuff
Bidiyo: Budurwa mai shekaru 23 tayi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89. Hoto daga @thesavoyshow
Asali: Instagram

Tayi martani ga masu sukarta tare da caccakar abinda tayi, wasu suna kiran budurwar da karuwa.

A bidiyon da aka wallafa a shafin @thesavoyshow a Instagram, budurwa ta yi magana kan yadda saurayinta wanda yanzu ya zama 'dan mijinta ya dinga cin amanartar da mata daban-daban har da kawayenta.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani bangare na bayaninta yace:

"Wato ana kirana da karuwa saboda na aura mahaifin tsohon saurayina, amma tsohon saurayina da ya dinga cin amantaa da mata daban-daban har da kawayena ba karuwa bane ko?"

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng