Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

  • Bidiyon wani jami'in 'dan sanda yana karbar cin hanci ba tare da boye fuskarsa ko nuna tsoro ba ya bayyana a dandalin sada zumunta
  • A kalaman jami'in dan sandan, yace baya son kananan canji, yafi son masu kauri wato manyan kudi ta yadda ko kama shi aka yi ya san hanci yaci da kyau
  • A bidiyon da masu ababen hawa suka nada na jami'in, an ji yana cewa hatta IGP da kwamandan shi sun san yana wannan harkar ta cin hanci

Bidiyon wani dan sanda kai tsaye ba tare da fargaba ba ya na amsar cin hanci a hannun jama’a ya bayyana a yanar gizo.

Da alamu masu wucewa ne a kan babban titin su ka dauki bidiyon.

Dan sanda
Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Dan sandan ya dakatar da su ne inda ya bukaci su ba shi “kudi mai kauri” cike da nuna iko da isa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

Kamar yadda dan sanda yace, ko sifeta janar na ‘yan sanda ya san yana amsar cin hancin daga hannun jama’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa kwamandansu ma ya umarce shi da ya tabbatar ya amshi kudi mai kauri yadda ko matsala aka samu, shi kwamandan zai iya kare shi.

A cewarsa, a bakin titin ne yake cin kasuwarsa yayin da masu wucewa da ababen hawa ne kwastomominsa da suke masa ciniki.

Yana sanye ne da kayan ‘yan sandan kuma bai yi wani kokari ba wurin rufe fuskarsa yayin da yake tattaunawa da masu wucewa ba.

Ga bidiyon a kasa:

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

A wani labari na daban, kwararren 'dan damben Turai, Sunny Edwards ya lakadawa wani wanda ya tsokane shi a Twitter mugun duka bayan ya tashi tun daga London zuwa wurin motsa jikinsa dake Sheffield domin su karasa rikicin da suka fara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Fab Tanga mai tsautsayin shan duka, ya biya har £110 inda yayi tafiyar mil 200 a jirgin kasa domin damben bayan kwanaki da suka samu sabani a kafar sada zumuntar zamanin.

Rikicin ya fara ne bayan Tanga ya wallafa a ranar Juma'a, 22 ga watan Yuli cewa: "Na yi alkawari, Sunny Edwards, nayi rantsuwa da rayuwata idan har baka ansa ni ba, safiyar gobe za ka ganni a gaban wurin motsa jikin ka tsakanin 11 zuwa 12. Idan ka bari na kashe kudin da zan ci abinci kuma baka bayyana ba, zan dinga yawo a Sheffield inda bayyana cewa kai rago ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng