Da duminsa: Bayan barazanar garkuwa da El-Rufai, 'yan ta'adda sun kai harin ban mamaki a Kaduna

Da duminsa: Bayan barazanar garkuwa da El-Rufai, 'yan ta'adda sun kai harin ban mamaki a Kaduna

  • Bayan barzanar da 'yan bindiga suka yi na cewa zasu sace Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, sun kai mummunan hari Millenium City
  • An gano cewa sun kwashe sa'o'i suna barna a daren Litinin inda suka sace tarin mutane har goma sha shida
  • A makonni uku da suka gabata, 'yan ta'addan sun kai farmakin yankin inda suka sheka kwamandan JTF tare da sace wasu

Kaduna - 'Yan ta'adda sun sake kai mummunan farmaki Millennium City dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da mazauna yankin.

A safiyar Talata, SaharaReporters ta gano cewa maharan sun kutsa yankin a daren Litinin inda suka kwashe sa'o'i suna aiki.

Labari da dumi
Da duminsa: Bayan barazanar garkuwa da El-Rufai, 'yan ta'adda sun kai harin ban mamaki a Kaduna
Asali: Original

A makonni uku da suka gabata, 'yan ta'addan sun kai hari Sabon Gero dake sabuwar Millennium City inda suka halaka kwamandan rundunar hadin guiwa da wani mazaunin yankin.

Kara karanta wannan

Kowa yana amfana da rashin tsaro, hatta gwamnati: Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga yayi fallasa

Sun kara da sace mutane 16 har da wani likita a abinda yayi kama da farmakin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya tace marigayin kwamandan JTF din ya bude wuta bayan hango 'yan bindigan da rashin sanin cewa sauran 'yan ta'addan sun zagaye shi.

"'Yan bindigan sun bude wuta kuma sun harba kwamandan a kafa inda yayi warwas. Daga nan suka harbe shi a kai inda suka fasa masa kai. Wani mazaunin yankin wanda aka harba, ya rasu ana hanyar kai shi asibiti," majiyar ta kara da cewa.

A sabon farmakin ranar Litinin, SaharaReporters ta gano cewa an sace mutane masu yawa.

Har a yayin rubuta wannan rahoton, rundunar 'yan sanda da hukumomin soji basu riga sun yi magana a kan farmakin ba.

Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

A wani labari na daban, fusatattun iyalan Fasinjojin da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa sun kewaye hedkwatar ma'aikatar sufuri ta tarayya, sun hana ma'aiakta shiga ofisoshin su.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan zanga-zangar na zuwa ne awanni 24 bayan wani bidiyo da ya bayyana ya nuna yan ta'addan na dukan fasinjojin da suka rage a hannun su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng