Dukan fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja: Iyalan waɗan da ke hannun yan ta'adda sun yi zanga-zanga a Kaduna
- Iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'adda suka yi garkuwa da su sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna
- Wakilin mu ya ziyarci wurin kuma masu zanga-zangar sun shaida masa suna nuna fushin su ga halin ko in kula da FG ta nuna
- A yau ne aka wayi gari a Najeriya da wani sabon bidiyo, wanda ya nuna yadda yan ta'adda ke dukan fasinjojin
Kaduna - A ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli 2022, iyalan fasinjojin da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja, sun yi zanga zanga a titin Nnamdi Azikwe Bypass, Kaduna.
Zanga zangar a cewar Aisha MS Utaz, sun yi ta ne domin nuna bacin ransu akan yadda gwamnati ta yi kunnen uwar shegu akan bukatar da yan bindigar suka nema kafin sakin fasinjojin, ba tare da kuma Gwamnatin ta samar da wata maslahar ba.
Da Dumi-Dumi: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar
Wakilinmu, Sani Hamza Funtua, wanda ya halarci taron zanga zangar, ya ruwaito cewa; matasan sun nuna takaicinsu kan yadda wani bidiyo da ya yi yawo a ranar Asabar, inda aka nuna yan bindigar na dukan fasinjojin da suka yi garkuwa da su, sakamakon gazawar Gwamnatin na cika masu bukatunsu.
Kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito, kwanaki 121 ke nan da yan bindiga suka farmaki jirgin kasa, da ke jigilar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi garkuwa da mutane da dama.
Hotunan zanga-zanga
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A sabon bidiyon da yan Najeriya suka wayi gari da shi yau Lahadi, ɗaya daga cikin fasinjojin ya yi kira ga ƙasashen duniya su kawo musu ɗauki tun da gwamnatin Najeriya ta gaza.
A cewarsa mutanen sun nemi bukatu da farko gwamnati ta gaza biya musu, yanzun sun samu yan uwansu kuma sun canza buƙatu amma gwamnati ta yi biris.
Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua
Abin da masu zanga-zangar ke cewa
Wakilin Legit.ng Hausa ya zanta da wata mata da mijinta ke hannun yan ta'adda. ta ce, "An saki bidiyo ana dukan bayin Allah, shin ba su da yanci ne? Gwamnati ta taimake mu ta fito mana da su in ba so take a nuna ana yanka su ba."
"Mu muka zaɓi wannan gwamnati amma yanzu ta zo tana zalintar mu, a fito mana da yan uwan mu, a fito mana da mazajen mu, iya abin da zan ce kenan."
Wani Muktar Abdulhamid ya shaida wa wakilin mu da ya yi tattaki zuwa wurin cewa ba'a kyauta musu ba kasancewar mahaifinsa na cikin fasinjojin.
Ya ce an saki bidiyo ana dukan iyayen su tamkar dabbobi yayin da shugabanni ke can da tsaro, wannan ba adalci bane inji shi.
A wani labarin kuma an kama wani ƙasurgumin mai garkuwa yana ɗaukar ma'aikata zasu sace mahaifin kwamishina a Neja
Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da ke shirin sace manyan mutane biyu a jihar.
Yayin bincike, wanda ake zargi Alhaji Bashiru ya amsa cewa yana shirin sace su ne saboda bashin kudin da yake bi.
Asali: Legit.ng