Najeriya Ta Samu Tsaro Domin Zuba Hannun Jari, Gwamnatin Buhari

Najeriya Ta Samu Tsaro Domin Zuba Hannun Jari, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayya ta ce akwai tsaro da kwanciyar hankalim zuba hannun jari a Najeriya ba kamar yadda wasu ke yaɗawa ba
  • Alhaji Lai Muhammed, ministan yaɗa labarai da Al'adu, ya ce daga zuwan Buhari, gwamnatinsa ta taɓa ko wane ɓangare da ta ɗauki alƙawari
  • Tattalin arziki, tsaro da yaƙar cin hanci da rashawa ne abu uku da gwamnatin ta ɗau alƙawari inji Lai kuma ta kama hanyar cika su

Lagos - Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce akwai kwanciyar hankalin zuba hannun jari a Najeriya duk kuwa da ƙoƙarin kashe kasuwa da masu hamayyar siyasa suka tsiro da shi.

Daily Nugerian ta rahoto cewa Ministan ya yi wannan furucin ne a wurin taron zuba hannun jari mai taken, "Tafiyar Afirka," wanda ƙungiyar UNICORN ta shirya a Legas.

Kara karanta wannan

Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki

Ministan ya ce wasu da ke kokarin maida hannun agogo baya na yaɗa karerayin cewa Najeriya ta faɗa dandalin yaƙi ko akwai tsattsauran ra'ayin addini a ƙasar.

Alhaji Lai Muhammed.
Najeriya Ta Samu Tsaro Domin Zuba Hannun Jari, Gwamnatin Buhari Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

Muhammed ya ce gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta hau kan mulki a 2015 bisa alƙawurran haɓaka tattalin arziki, yaƙar matsalar tsaro da kuma kawo ƙarshen cin hanci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan ya ce:

"An zaɓe mu ne kan ginshiƙai uku, tatattalin arziki, tsaro da cin hanci, a waɗan nan ɓangarori uku ina tabbatar muku da cewa babu wanda ba mu tanƙwara ba duk da ƙalubalen da muke fuskanta."

Wane nasarori gwamnati ta samu a bangaren tsaro?

Da yake tsokaci game da tsaron ƙasa, Ministan ya ce ƙungiyar Boko Haram da ta kwace iko da yankuna da dama a arewa maso gabas ƙafin zuwan wannan gwamnatin an karya ta, haka nan kuma an tarwatsa jagorancin ISWAP.

Kara karanta wannan

Peter Obi ba zai kai labari ba a 2023, kaso 90% na yan arewa basu Soshiyal Midiya, Atiku ya magantu

Ya ce yan ta'adda 51,000 suka miƙa wuya a watanni ukun farko na wannan shekarar kaɗai, yayin da gwamnati ta maida hankali wajen gyara da gina garuruwan da yan ta'addan suka lalata.

Domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya, wannan gwamnatin ta zama ta farko da ta ɓullo da tsarin yi wa makiyaya wurin kiyo, Inji Lai don haka ya yi kira ga sauran gwamnoni da basu yi ba su aiwatar da shirin gwamnati.

"Muna kokarin daƙile ayyukan yan bindiga ta yadda muka yi wa Boko Haram da ISWAP, abu ne na lokaci yan bindiga zasu zama tarihi."

Tattalin arziƙi

Game da tattalin arziƙi kuma, Lai ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar rage dogaro da kayan da ake shigowa da su. A cewarsa yaƙin Rasha-Ukarine da annobar Korona ta yi illa ga kowane tattalin arziki.

Cin Hanci da rashawa

A ɓangaren yaƙi da cin hanci kuwa, Ministan ya ƙara da cewa daga watan Janairu zuwa Disamba, 2022, an kwato dukiyar gwamnati biliyan N152bn; Dalar Amurka miliyan 386, Pound na ƙasar Birtaniya 1.1 miliyan, Yuro 157,000, da Riyal na Saudiyya 1.7 da dai sauran su.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankaɗo yadda Dakataccen Akanta Janar ya karɓi Biliyan N15bn na goro don saurin biyan jihohi 9 wasu kuɗaɗe

Ya ce baki ɗaya kuɗaɗem da gwamnati ta kwato sun tafi ne wajen gina manyan ayyukan raya ƙasa a sassan Najeriya.

A wani labarin kuma Yan ta'addan da suka farmaki jirgin ƙasan Kadun zuwa Abuja sun saki sabon Bidiyon yadda suke azabtar da fasinjojin dake tsare

Ƙungiyar yan ta'adda waɗan da suka kai hari kan jirgin ƙasa da ke aiki tsakanin Abuja-Kaduna sun yi baranar tarwatsa Najeriya baki ɗaya.

A wani sabon Bidiyo da yan ta'adda suka sake, sun nuna yadda Fasinjojin jirgin kasa da ke tsare a hannun su ke rayuwa da yadda suke azabtar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262