An Gurfanar Da wani Likitan Birtaniya Da Laifin Hada Baki Da Ekweremadu Kan Girbin Koda
- An gurfanar da wani likita mai suna Obinna Obeta da laifin hada kai da Senata Ike Ekweremadu da shirin girbin koda wani yaro
- Ekwerenmadu da Matar sa sun ya shirya cire kodar David domin a ba wa diyarsu da take fama da ciwon koda
- David ya ki amincewa a cire kodar sa bayan da aka yi masa gwaje-gwaje a asibitin kyauta na Royal da ke Hampstead
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Birnin Landan - Wani Likitan da ke birnin Landan ya hada kai da Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, a Burtaniya da shirin girban kodar wani dan Najeriya mara galihu.
Obinna Obeta, mai shekaru 50, dake zama a Landan, ya bayyana a kotun Majistare ta Bexley a ranar 13 ga watan Yuli, bisa zargin hada baki da Ekweremadus don shirya tafiyar Ukpo Nwamini David mai shekaru 21 daga Najeriya zuwa Birtaniya.

Kara karanta wannan
Babu boye-boye: ‘Dan takaran Shugaban kasa ya Jero Duk Abin da ya Mallaka a Duniya
Ana zargin Obeta da hada baki da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya da kawo David Burtaniya da nufin girbin sassan jikin sa.

Asali: Facebook
Zargin ya zo ne a karkashin dokar bautar zamani, a cewar jaridar The Mail of London.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Masu gabatar da kara sun ce Ekweremadus ya shirya cire kodar David domin a bai wa diyarsu mai fama da ciwon koda.
An ce David ya ki amincewa da aikin ne bayan da aka yi masa gwaje-gwaje a asibitin kyauta na Royal da ke Hampstead, a London.
Masu gabatar da kara na kuma zargin Ekweremadus da daukar David a matsayin bawa kafin ya tsere ya tafi ofishin 'yan sanda na Staines da ke Surrey.
Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, Ta Ayyana Kyandar Biri a Matsayin Wanda Ke Bukatar Daukin Gaggawa a Duniya

Kara karanta wannan
Biki Ake Na Manya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu
A wani labari kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a ranar Asabar ta bayyana cutar Kyandar Biri a matsayin wanda ke bukatar daukin gaggawa a duniya, rahoton The Punch.
Hukumar lafiyar ta Duniya ta ce ta dauki mataki mafi karfi kan cutar da ke yaduwa, hakan yasa kwayar cutar ta zama abin da ke bukatar gaggawa a kasashen duniya.
Asali: Legit.ng