Mayakan Boko Haram 5 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Jihar Borno
- Wasu Mutane da aka zargi mayakan Kungiyar Boko Haram ne tare da kwamandan su, sun mika wuya ga sojoji a jiharBorno
- Bincike ya nuna yanta'adan da suka mika wuya ga sojoji sun daga sabuwar hedikwatar kungiyar Boko Haram dake shahara
- Kwamandan Rundunar Sojoji na Operatio Hadin Kai ya ce sama da mahara 67,000 ne suka mika wuya ga sojoji ya zuwa yanzu
Jihar Borno - Wasu mutane biyar da ake zargin 'yan Boko Haram ne da suka hada da Mallam Isa, kwamanda a kungiyar, sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya a Borno. Rahoton THE CABLE
A cewar Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ‘yan tada, yace sun mika wuya ne a ranar 22 ga watan Yuli ga sojojin bataliya ta 73, na Operation Hadin Kai.
Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano
“A ranar Juma’a, ne sojojin bataliyan Cashew da aka tura Shuwa suka karbi ‘yan ta’addar Boko Haram biyar da suka mika wuya.
“Bincike na farko ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga Gazuwa, wata sabuwar hedikwatar kungiyar Boko Haram a shahara, mai tazarar kilomita 8 zuwa karamar hukumar Bama" inji shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makama ya ce daga baya mata da kananan yara 29 suka fito suka mika wuya ga sojojin yayin da suka ga ba a kashe yan ta’addan da suka fara mika wuya ba.
Christopher Musa, kwamandan rundunar Hadin Guiwar Arewa Maso Gabas na Operation Hadin Kai, ya ce sama da mahara 67,000 ne suka mika wuya ga sojoji ya zuwa yanzu.
A watan Afrilun 2022, mutane 10 da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Borno.
Bana garkuwa da mutane kashewa kawai nake yi – shugaban ‘yan ta’addan Zamfara
A wani labari kuma, Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Ada Aleru, wanda a kwanan nan aka nada masa sarautar Sarkin Fulanin Yandoton Daji (shugaban Fulani a Yandoton Daji) a wata sanarwa mai ban tsoro, ya ce ba ya sace mutane sai dai ya kashe su. Rahoton PREMIUM TIMES
Nadin sarautar Aleru, wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a Tsafe da Faskari a jahohin Zamfara da Katsina, ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng