Yan Bindiga sun Sace Wa Makiyaya Shanu 2,000 A Sakkwato
- Yan Bindiga sun yi wa wasu makiyaya yan asalin Jihar Kebbi satar shanu 2,000 a Jihar Sakkwato
- Shugaban Miyetti Allah na jihar Kebbi ya ce yana da kwarin gwiwa jami’an tsaro za su kwato shanun da yan bindiga suka sace
- Dabi’ar makiyaya ne kai dabbobin kiwo jihar Neja a kowani shekara sannan su dawo da su gida lokacin damina inji Shugaban Miyetti Allah
Jihar Sakkwato - Yan Bindiga sun yi wa wasu makiyaya yan asalin Jihar Kebbi satar shanu 2,000 a Jihar Sakkwato. Rahoton Aminiya.Daily.Trust
Yan Bindigan sun tare Makiyayan ne a lokacin da suke kan hanyar su na komawa gida inda suka kwace musu dabobi suka arce dasu zuwa maboyar su dake cikin dajin Zamfara
Sakataren Kungiyar Makiyayan Miyetti Allah na Jihar Kebbi, Abubakar Bello Bandam, ya shaida wa manema labaru cewa:
“Makiyayan sun kawo mana rahoton cewa an sace musu shanun su sama da 2,000 a safiyar Laraba, inda aka kora su cikin dajin jihar Zamfara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Makiyayan ’yan asalin Jihar Kebbi ne, amma a kauyen Kuchi na Jihar Sakkwato aka tare su, a hanyarsu ta dawowa daga Borgu, a Jihar Neja aka musu fashin.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jihar Kebbi Bello Bandam, ya ce makiyayan sun tsere sun bar dabbobin su a lokacin da suka hango maharan dauke da muggan makamai domin tsira da rayuwarsu.
Daga nan su kuma ’yan bindigar suka arce da dabbobin gaba daya zuwa maboyarsu da ke dajin Zamfara.
Ya ce, dabi’a ce na makiyaya su kai dabbobin kiwo yankin Borgu a jihar Neja a kowani shekara, sannan su juyo da su gida lokacin damina.
Abubakar Bello Bandam, ya ce yana da yakinin jami’an tsaro za su kwato musu dabbobin su ,don sun gaggauta kai wa ’yan sanda rahoton fashin da aka musu.
Matsalar Tsaro: Kashi 70 na wadanda aka kashe a watan Yuni a Arewa suke
A waji labari kuma, Wani Bincike game da harkar tsaro a Najeriya ya nuna kashi 75 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga a watan Yuni a Arewacin Najeriya suke. rahoton BBC
Sabuwar binciken da kamfanin Beacon Consulting Limited ta fitar akan harkar tsaro na watan Yuni, ya nuna cewa an kai harin yan bindiga sau 338 a fadin kasar kuma an sace mutane 651.
Asali: Legit.ng