Haɗin kan Najeriya da tsaro zan sa gabana ko bayan na bar mulki, Buhari

Haɗin kan Najeriya da tsaro zan sa gabana ko bayan na bar mulki, Buhari

  • Shugaban ƙasa Buhari ya ce ko bayan ya sauka daga mulki zai fi ba tsaro da haɗin kan ƙasa nuhimmanci a harkokinsa
  • Buhari, wanda ya karɓi bakuncin masu ruwa da tsakin APC, ya gode musu bisa halin dattakon da suka nun a tafiyar da jam'iyya
  • Abubuwa biyu da Buhari ya ambata watau tsaro da haɗin kai su suka zama ƙarfen kafa da ya addabi gwamnatinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammasu Buhari, ya ce haɗin kai, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar nan zai sa a gaba ko bayan ya bar Ofishin shugaban ƙasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyarsa ta APC karkashin jagorancin shugaban jam'iyya na ƙasa, Sanata Abudullahi Adamu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ba zai kai labari ba a 2023, kaso 90% na yan arewa basu Soshiyal Midiya, Atiku ya magantu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Haɗin kan Najeriya da tsaro zan sa gabana ko bayan na bar mulki, Buhari Hoto: Buharisallau1
Asali: Twitter

Shugaban, wanda ya nuna gamsuwarsa da hanyar da APC ta ɗakko ya gode wa wakilan, "Bisa rawar da suka taka har ta kai ga tsayar da ɗan takara da mataimaminsa a zaɓen shugaban ƙasan da ke tafe shekara mai kama wa."

"Ina ƙara gode muku bisa rawar da kuka taka tun daga matakin farko, na ɗaya kan shirin babban taron mu na ƙasa wanda ya gudana farkon wannan shekarar, na baya kuma zaɓen fidda gwanin mu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kun haɗa zuciyoyin ku wuri ɗaya, kuna son abu mai kyau ga jam'iyya tare da ɗan takarar mu ya bayyana ta hanyar ingantacciyar hanya."
"A wurin mu haɗin kan jam'iyya ne a sahun gaba, da kuma burikan dake zuciyar mu su biyo baya. Naji daɗin yadda kuka karkata kan abinda ya fi dacewa sama da son zuciyoyin ku."

- Buhari.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankaɗo yadda Dakataccen Akanta Janar ya karɓi Biliyan N15bn na goro don saurin biyan jihohi 9 wasu kuɗaɗe

Shin Buhari ya yi tsokaci kan abokin takarar Tinubu?

Idan baku manta ba lokacin da aka gabatar masa da ɗan takarar mataimaki, Sanata Kashim Shettima, Buhari ya ce zai ɓoye kalamansa har sai ranar da zai miƙa musu mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 a filin Eagle Square.

"Ina nan a akan bakata," Inji shugaban ƙasan yana mai kallon mambobin, waɗan da duk sun cancanci samun wannan matsayin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Buhari a wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar, ya nuna kwarin guiwarsa cewa Shettima ba zai ba APC da yan Najeriya kunya ba.

A wani labarin kuma gwamnoni huɗu dake shirin ficewa daga PDP sun gana da juna, sun faɗi matakin da suka dauka na karshe

Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kwata ta yi ajalin wani matashi ɗan shekara 25, Ghaddafi Saleh, a Kano

Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262