Laura Nuttall ta kammala digiri shekaru 4 bayan likitoci sun ce mata sauranta watanni 12 ta rayu
- Laura Nuttall, wata mata mai shekaru 22, an gano tana da larurar glioblastoma multiforme, nau'in ciwon daji mafi illa ga kwakwalwa, kuma an ce shekara guda ya rage ta rayu
- Sai dai Laura ta tsallake yayin da ta jingine makaranta ta fara jinya da neman magani ciki har da tiyatar cire ciwon
- Ba tare da wata matsala ba, budurwar ta kammala karatunta daga baya a Jami'ar Manchester inda ta karanci siyasa, falsafa da tattalin arziki
Laura Nuttall, mai shekaru 22 ta kammala digiri a fannin siyasa, falsafa, da tattalin arziki ba tare da wata matsala ba.
A 2018, an gano Laura tana dauke da wani nau'in ciwon daji guda 8 bayan an gano tana dauke da larurar glioblastoma multiforme; wani nau'in ciwon daji mafi illa ga kwakwalwa.
Laura ta bar makaranta don neman magani
Daga baya dai da cuta tayi tsanani, Laura ta bar makaranta domin nemo magani. Sai dai likitoci sun ce za ta rayu ne na tsawon watanni 12 kawai a lokacin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai Laura ta tsallake wannan wa'adi na likiroci, har zuwa kammala makaranta bayan da ta dukufa ga jinya sosai, ciki har da yi mata wata tiyata.
Ta kammala karatu daga baya a Jami'ar Manchester ta Ingila. Da take mayar da martani, budurwar ta shaida wa BBC cewa abin dai ga shi kamar almara.
A kalamanta:
"Likitoci na sun ce min ba zan koma jami'a gaba daya ba, ban yi tunanin zan kammala karatu ba, amma ga ni, a karshe dai, a shekara ta farko, ban tsammani ko zan iya kaiwa ga nasarar kammala karatun ba, kada ku damu don na sami 2: 1."
Murnar biki kamar ba za a mutu ba
Dangin Laura sun shiga biki yayin da ta kammala digirinta ba tare da wata matsala ba. Mahaifiyarta ta cika da farin ciki matuka.
Mahaifiyar mai suna Nicola ta ce:
"An gaya wa Laura cewa tana da kusan shekara guda ya rage mata na rayuwa kuma ba za ta koma jami'a ba kwata-kwata, don haka ganin ta kammala karatun ta abu ne mai ban mamaki.
"Na san irin wahalar da ta sha ta yi don samun digirin ta tare da sauyin jini, tiyata da neman magani, kuma wannan rana ta kasance bikin hakikanin kokarinta."
Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dakon Kaya Da Sayar Da Soyayyen Nama Na Ke YI: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo
A wani labarin, wani matashi dan Najeriya mai suna Dwomoh Emmanuel, ya tafi TikTok domin nuna sana'ar da ya ke yi akasin abin da ya karanta yayin digiri a jami'a.
Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Saka Jaruman Fim A Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka
Matashin da ya yi digiri a bangaren kididdiga, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana daukan kaya sannan yana sayar da soyayyen kaza a wani shago.
Mutumin ya dauki babban jaka a kansa. Wani sashi na bidiyon ya nuna shi yana soya wani abu da ya yi kama da fukafukin kaza.
Asali: Legit.ng