Hukumar kula da Hadura FRSC tana son a nada magajin Boboye daga cikin jami’anta

Hukumar kula da Hadura FRSC tana son a nada magajin Boboye daga cikin jami’anta

  • Ciyaman din hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ya yi kira da a nada sabon shugaban FRSC daga cikin jami’an hukumar maimakon dauko wani daga wajen
  • Boboye Oyeyemi yana daya daga cikin tsirarun jami’an da suka kafa hukumar Federal Road Safety Comission FRSC a Najeriya
  • Dokta Boboye Oyeyemi ya taka rawan gani wajen samar da gidaje da filaye masu araha ga ma’aikatan hukumar FRSC

Abuja - Ciyaman din hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Bukhari Bello, ya yi kira da a nada sabon shugaban FRSC daga cikin jami’an hukumar maimakon dauko wani daga wajen. Rahoton Dail Trust

Ya bayyana haka ne a wani taro da hukumar FRSC ta gudanar a ranar Alhamis a Abuja inda ya ce:

"Shugaban hukumar mai barin gado, Boboye Oyeyemi, ya taka rawar gani sosai don haka akwai bukatar a nada wani daga cikin su domin daurawa inda ya tsaya.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

“Wani gagarumin aiki da Dokta Boboye Oyeyemi ya dauka kuma ya aiwatar, shine samar da gidaje da filaye masu araha ga ma’aikatan hukumar.
Boboye
Hukumar kula da Hadura FRSC tana son a nada magajin Boboye daga cikin jami’anta FOTO Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi, Shugaban hukumar FRSC mai barin gado, Boboye Oyeyemi ya ce:

"lasisin tuki na dijital zai fara aiki nan ba da jimawa ba.

Ya kuma ce ana kokarin kara yawan masu rajista a kan lasisin tuki (NDL) ta hanyar samar da kayan aikin hannu da za a tura ga masu neman NDL cikin sauki.

Boboye Oyeyemi shine jami'i na karshe daga cikin jami'ai bakwai da suka fara aiki a hukumar FRSC a jihar Oyo tare da Farfesa Wole Soyinka a matsayin shugaba na farko a lokacin da aka kafa hukumar a 1988 da yayi ritaya.

Daga karshe, shugaban Hukumar Kiyaye Hadura FRSC Boboye Oyeyemi yayi ritaya daga aiki

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban SSS ya caccaki Kudirin hana Hawa Babura a Najeriya

A wani labar kuma, Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa Federal Road Safety Comission (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya yi ritaya daga aiki. Rahoton INDEPENDENT

Ranar Juma'a 19 Yuni za a mishi Faretin fita daga aiki (Pull Out Parade) a Abuja kafin a sanar da wanda zai maye gurbin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa