Tsohon shugaban SSS ya soki kudirin hana hawa babura a Najeriya
- Wani tsohon darakta a hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) Mike Ejiofor ya soki kudirin gwamnatin tarayya na yiwuwar hana amfani da babura a fadin kasar.
- Malami, ya shaida wa manema labarai cewa gwamnati na duba yiwuwar hana hawa babura da ayyukan hakar ma’adanai don dakile matsalar tsaro a kasar
- Mike Ejiofor ya ce hana hawa babura a fadin kasar zai yi mummunan tasiri ga zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta fada a ranar Alhamis cewa tana duba yiwuwar hana hawa babura da ayyukan hakar ma'adanai a fadin kasar domin dakile kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Rahoton Premium Times
Wani tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) Mike Ejiofor ya caccaki yunkurin gwamnatin tarayya na yiwuwar hana amfani da babura a fadin kasar.
Mista Ejiofor ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels
Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis, cewa gwamnati na duba yiwuwar hana hawa babura da ayyukan hakar ma’adanai domin dakile tabarbarewar tsaro a kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malami Yace :
"Zartar da dokar hana amfani da babura da ayyukan hakar ma'adinai zai rage samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da wasu sassan kasar na gudanar da ayyukansu ne ta hanyar amfani da babura.
Mista Ejiofor ya yi zargin cewa irin wannan shawarar za ta yi mummunan tasiri ga zamantakewa da tattalin arziki ga mutane.
“Idan aka hana amfani da babura a yankunan da ake fama da hare-haren ta’addanci mutum zai fahimci kudirin gwamnati, amma hana hawa Babura a kasar baki daya, ina ganin zai haifar da matsaloli da dama na zamantakewa da tattalin arziki.
Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano
Matsalar Tsaro: Kashi 70 na wadanda aka kashe a watan Yuni a Arewa suke
A wani labari kuma, Wani Bincike game da harkar tsaro a Najeriya ya nuna kashi 75 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga a watan Yuni a Arewacin Najeriya suke, rahoton BBC
Sabuwar binciken da kamfanin Beacon Consulting Limited ta fitar akan harkar tsaro na watan Yuni, ya nuna cewa an kai harin yan bindiga sau 338 a fadin kasar kuma an sace mutane 651.
Asali: Legit.ng