Hoton Sunan 'Allah' Da Wani Musulmi Ɗan Najeriya Ya Gani A Dafaffen Nama Da Ya Siya A Abuja

Hoton Sunan 'Allah' Da Wani Musulmi Ɗan Najeriya Ya Gani A Dafaffen Nama Da Ya Siya A Abuja

  • Wani mutum dan Najeriya mai suna Wushishi Habibu mazaunin Abuja ya yi ikirarin ganin sunan Allah rubuce a jikin nama da ya siyo daga wurin cin abinci
  • Wushishi ya bayyana cewa tsakaninsa da Allah bai taba yarda da irin labaran abubuwan ban mamaki irin wannan a baya ba amma gashi yanzu Allah ya nuna masa karara
  • Ya ce ya tafi ya siyo abincin rana ne daga wani wurin cin abinci mai suna Abdullahi Aisha ya koma ofis ya bude zai fara cin nama kwatsam sai ga rubutun sunan Allah

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Wani dan Najeriya mazaunin birnin tarayya Abuja, Wushishi Habibu, ya yi ikirarin cewa ya ga sunan 'Allah' a rubuce a jikin nama da ya siya a wurin cin abinci a ranar Laraba 20 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Duk da mallakar miliyoyi, attajirin dan dambe ya ce saura kiris ya mutu

Sunan Allah Ya Bayyana a Dafafen Nama a Abuja
Wani Musulmi Dan Najeriya Ya Yi Ikirarin Ya Ga Sunan 'Allah' a Jikin Nama Da Ya Siya. Hoto: Wushishi Habibu.
Asali: Facebook

Ya rubuta:

"Tsakani na da Allah da ya hallice ni, yanzu na ga wannan a yayin da na ke cin abincin rana a ofis. Ban taba yarda da irin wannan da na gani a baya ba amma Allah ya nuna min shi karara a yau. Na siya abinci daga wurin cin abinci na Abdullahi Aisha kuma bayan na koma inci sai naga sunan Allah a rubuce a jiki. Allah da girma yake.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin wasu yan Najeriya kan abin ban mamakin:

Gimbiyan Bosso:

"Allahu Akbar, alama ce ta karshen duniya. Allah ya fada cewa za mu rika ganin sunayensa a wuraren da ba mu yi tsammani ba. Allah ya mana jagora. Ammen."

Abdullahi Isiyaku ya ce:

"Ni ma shaida ne, zan iya tabbatarwa na gani."

Zainab Khalil Ismaila:

"Allah mai girma ne kuma zai cigaba da kasancewa mai girma."

Kara karanta wannan

Ban dai ji dadi ba: Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe malamin Kirista a Kaduna

Zainab Ibraheem cewa ta yi:

"Allahu Akbar, alamun karshen duniya, Allah ya yafe mana kurakurenmu."

Rabi Bello ta ce:

"Allah ya yafe mana kurakuren mu kuma ya bamu nasara da karshe mai kyau."

Rabiah Ahmad ta rubuta:

"Allahu Akbar na so da na zo mun ci naman tare".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164