Almundahar N109bn: EFFC Za Ta Gurfanar Da Daktaccen Akanta Janar, Idris, Ranar Juma'a

Almundahar N109bn: EFFC Za Ta Gurfanar Da Daktaccen Akanta Janar, Idris, Ranar Juma'a

  • Ahmad Idris, dakataccen Akanta Janar na Tarayyar Najeriya zai gurfanar a gaban kuliya a ranar Juma'a 22 ga watan Yulin 2022
  • Tun a watan Mayu ne hukumar yaki da rashawa na EFCC ta kama Ahmed a Jihar Kano kan zarginsu da almundahar kudi bayan ta gayyaci shi ya ki zuwa
  • EFCC tana tuhumar Ahmed ne da wani Geofrey Akindele da Mohammed Kudu Usman da lafin cin amana da karkatar da zunzurutun kudi Naira biliyan 109

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ta ce za ta gurfanar da Ahmed Idris, dakataccen Akanta Janar na tarayyar Najeriya, a kotu a ranar Juma'a.

A watan Mayu ne aka kama Idris a Kano bayan ya ki amsa gayyatar da hukumar ta masa don amsa tambayoyi kan zargin almundahar Naira biliyan 80.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano

Ahmed Idris.
Badakalar N109bn: EFFC Za Ta Gurfanar Da Daktaccen Akanta Janar, Idris, Ranar Juma'a. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan kwana biyu, ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, Zainab Ahmed ta dakatar da Idris ba tare da albashi ba.

A cewar sanarwar da Wilson Uwujaren, kakakin hukumar ya fitar a ranar Alhamis, ana fatan gurfanar da Idris tare da 'Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman', yayin da wani kamfani - Gezawa Commodity Market and Exchange Limited - shima na cikin tuhumar.

EFCC ta ce Idris da sauran mutanen da aka yi kararsu tare ana tuhumarsu ne da aikata laifuka 14 masu alaka da sata da laifin cin amana ta kudi Naira biliyan 109.5.

Daya cikin zargin da ake masa na cewa:

"Kai, Ahmed Idris din yayin ka ke Akanta Janar na Tarayya da Godfrey Olusegun Akindele yayin da ya ke hadimi na Akanta Janar na Tarayya tsakanin watan Fabrairu da Nuwamban 2021, an damka muku amanar wani kadara wato kudi N84,390,000,000 (Biliyan Tamanin da hudu, miliyan dari uku da casa'in) kuka ci amana kan kudin inda ka karkatar da kudin ta hannun Geofrey Olusegun Akindele karkashin kamfanin Olusegun Akindele & Co, kuma ka aikata laifi karkashin sashi na 315 na dokar Penal Code Act Cap 532 na dokokin tarayyar Najeriya, 1990."

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan Hadiza Buhari cikin iyalan Malami sun kayatar, uwargida ta karbeta hannu bibbiyu

Tsohon AGF Ya Karɓi Biliyan N15bn Don Gaggauta Biyan Jihohin Ɗanyen Mai Kuɗaɗensu, EFCC

A gefe guda, kun ji cewa Akanta Janar na ƙasa (AGF) da aka dakatar, Ahmed Idris, ya karɓi biliyan N15bn ta bayan fage domin ya gaggauta biyan jihohi masu fitar da ɗanyen mai kason da ake ware musu.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'adi (EFCC) ta ce dakataccen AGF ɗin ya karɓi kudin ne a matsayin toshiyar baki domin saurin tura wa jihohin guda 9 ƙaso 13% da ake ware musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164