Duniya ba matabbata ba: Duk da mallakar miliyoyi, attajirin dan dambe ya ce saura kiris ya mutu

Duniya ba matabbata ba: Duk da mallakar miliyoyi, attajirin dan dambe ya ce saura kiris ya mutu

  • Shahararren dan wasan dambe, Mike Tyson, ya bayyana cewa saura masa kwanaki kadan a nan gidan duniya
  • Duk da mallakar miliyoyi, attajirin dan dambe ya ce babu wata tsiya a duniya domin dole kowa ya barta wata rana
  • Tyson ya ce yawan kudi na sa mutum ya yi tunanin yana da dukkan kariya alhalin ba haka abun yake ba a zahirin gaskiya

Attajiri kuma shahararren dan wasan dambe, Mike Tyson ya bayyana cewa yana iya mutuwa nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a shirinsa mai taken ‘Hotboxin’ with Mike Tyson,’ tsohon zakaran dan wasan damben ya kuma bayyana cewa yana shan gwagwarmaya tare da matarsa, duk da kasancewarsa hamshakin mai kudi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kun cika taurin kai: Gwamnatin Buhari ta caccaki ASUU, ta ce su suka aje dalibai a gida

Mike Tyson
Duniya ba matabbata ba: Duk da mallakar miliyoyi, attajirin dan dambe ya ce saura kiris ya mutu Hoto: marca.com
Asali: UGC

Shafin LIB ta rahoto cewa yake jaddada cewa yana ganin mutuwarsa na kara matsowa, Tyson ya ce:

“Dukkanmu za mu mutu wata rana, ko shakka babu. Idan na kalli madubi, Sai na ga wadannan yan kananan dabbon da ke kan fuskata, sai nace, ‘Lallai. Wannan na nufin lokacin mutuwata na kara gabatowa, nan kusa kadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kudi baya nufin wata tsiya a gare ni. A koyaushe ina fadama mutane haka. Suna tunanin kudi zai sanya su farin ciki, ba su taba samun irin wannan kudin ba, saboda idan ka taba ba wanda zai iya sonka da gaskiya. Ta yaya zan furta soyayya alhalin kana da dala biliyan 500 a banki?”
"Ma'anar tsaro ta karya, ka yi imani cewa babu abin da zai iya faruwa. Ba ka yarda cewa bankunan za su iya rushewa ba. Ka yarda cewa ka fi karfin komai idan kana da kudi da yawa, wanda ba gaskiya bane. Wannan ne dalilin da yasa a kullun nake cewa kudi kariya ce ta karya.”

Kara karanta wannan

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa mai kudin duniya, Elon Musk, ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter wanda ya girgiza mabiyansa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, yana mai cewa ya kusa mutuwa.

Koda dai bai bayar da cikakken bayani kan halin da yasa shi fadin haka ba, mai kudin ya nuna rayuwarsa na gab da zuwa karshe.

Ya rubuta: "Idan na mutu a cikin yanayi mai ban mamaki, ina alfahari da sanin ki/ka."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng