Hotunan soyayyar wata budurwa da matashi dan shekara 18 sun girgiza intanet

Hotunan soyayyar wata budurwa da matashi dan shekara 18 sun girgiza intanet

  • Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 20 ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ta nuna waye saurayinta
  • Ta yada wani bidiyo mai ban sha'awa da ta yi tare da saurayin nata mai shekaru 18, tana kwatanta kananan yara maza a matsayin wadanda suka fi dadin sha'ani
  • A cewar budurwar, lokaci ya yi da mutane za su kawar da ra’ayin alakar tsofaffi maza da ‘yan mata a rayuwar soyayya

Yayin da mutane da yawa ke ganin ya dace mata su gina alaka da maza masu shekaru, wata 'yar Najeriya ta zo da sabon salo a irin nata ra'ayin.

Budurwar ‘yar Najeriyar mai shekaru 20 kwanan nan ta tafi shafin TikTok don nuna alfahari da saurayin ta mai shekaru 18 kuma ta sa mutane da yawa suna ta magana a kai.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari zai kashe wa 'yan Najeriya N6.72trn a matsayin tallafin man fetur

'Yar Najeriyar mai shekaru 20 ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ta nuna saurayinta a cikin wani bidiyo.

Yadda budurwa ta yi wuff da matashi mai shekaru 18
Yara sun fi dadin harka: Hotunan soyayyar budurwar da ta auri dan shekara 18 | Hoto: TikTok/@iam_octavia2
Asali: UGC

A cikin faifan bidiyon da ta yada, budurwar da sauranyin nata sun girgiza jama'a da irin kayan da suka sanya mai kama daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyon na daban, ta bayyana samari masu kananan shekaru a matsayin mafi dadin mu'amala kuma ta bukaci mutane da su kawar da ra'ayin da ake yadawa cewa dole maza masu shekaru ne kawai za su iya neman mata masu kananan shekaru.

A cewarta:

"Muna bukatar mu canza wannan ra'ayi na maza masu manyan shekaru da 'yan mata."

Da take mayar da martani kan ko wanene daga cikinsu ya fara neman wani, budurwar ta bayyana cewa da gaske yaron ne ya fara nemanta.

Martanin jama'a a soshiyal midiya

PriestParzival ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Kurmus A Gobarar Da Ta Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jami'ar BUK

"Na gode, wasu suna ganin shekaru a matsayin matsala, wasu kuma suna da fahimtar cewa shekaru ba komai bane."

okaforchibuezeemm yace:

"Allah yaushe zan samu irin wannan budurwa, ba ina nufin kowace tarkace ba fa, KAI, ina son abin da nake gani yanzu."

1nqgx ya ce:

"Yawancin 'yan matan da na nema sun fi ni a shekare, amma ba wanda zai iya ganewa."

Ag✓ BSD ya ce:

"Amma fa kun ba da sha'awa, Haka nake a da ni da abokiyar zama ta, ta girme ni."

PeaceSpyce ya ce:

"Idan dai yana da kamun kai kuma kina girmama shi .... hakan ya yi, ku ji dadinku kawai."

Hotunan ƙasaitaccen shagalin auren kwaɗi da aka shirya a India don roƙon ruwa, an yi ruwan sama washegari

A wani labarin, wata kungiyar mutane a birnin Gorakhpur dake Indiya sun shirya kasaitccen bikin kwadi biyu domin kiran ruwa bayan watannin da suka kwashe suna fama da rashin ruwan sama wanda ya janyo tsananin zafi.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta

Kungiyar sun samu kwadi biyu a ranar 19 ga watan Yuli kuma sun yi bikin domin farantawa ubangijin ruwa Indra, rai.

Indian Express sun rahoto cewa, sun tirsasa kwadin biyu auren juna a matsayin wani bangare na tsafin duk da kokarin da suka dinga na ganin amarya da angon tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.