Wani matashi ɗan shekara 25 ya faɗa kwata a Kano, Allah ya masa rasuwa

Wani matashi ɗan shekara 25 ya faɗa kwata a Kano, Allah ya masa rasuwa

  • An gano wani matashi dan shekara 25, Ghaddafi Saleh, da ya faɗa Kwata a kan hanyar Zariya, yankin Tarauni a jihar Kano
  • Jami'an hukumar kwana-kwana sun yi gaggawar kai masa ɗauki, suka tsamo shi cikin mawuyacin hali, daga baya ya cika
  • A ranar Lahadi da ta gabata, an yi wani mamakon ruwa kamar da bakin kwarya na tsawon lokaci a Kano, ana ganin lamarin na da alaƙa da ruwan

Kano - Wani matashi ɗan shekara 25 a duniya, Ghaddafi Saleh, ranar Laraba, an tabbatar da ya rasu jim kaɗan bayan tsamo shi daga cikin kwata cikin mawuyacin hali.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya magantu a Kotu

Taswirar jahar Kano.
Wani matashin ɗan shekara 25 ya faɗa kwata a Kano, Allah ya masa rasuwa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daily trust ta rahoto Kakakin hukumar ya ce:

"A yau Laraba 20 ga watan Yuli, 2022, mun samu wani kiran gaggawa daga Malam Abdulƙadir, da misalin ƙarfe 7:26 na safe. Ya faɗa mana cewa wani mutumi ya faɗa Kwata a yankin Tarauni, kan hanyar Zariya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki suka ɗauka bayan samun rahoton?

Bayan samun wannan rahoton, Abdullahi ya ƙara da cewa nan take suka haɗa tawagar jami'ai da ke kan aiki kuman sun dira wurin da misalin ƙarfe 7:34.

Da zuwansu a cewar kakakin hukumar kashe gobaran, suka gano wani mutum da bai wuce shekara 25 ba mai suna, Ghaddafi Saleh, a cikin Kwata.

Abdullahi ya ce mutumin, wanda aka tsamo cikin mawuyacin hali, ya ƙarasa rasuwa daga baya kuma tuni aka miƙa gawarsa ga Insufecta Bashir Abdullahi na caji ofis ɗin hanyar Zariya.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 10 a jihar arewa

Meya haddasa faɗawar matashin cikin kwata?

Bayanai sun nuna cewa ana tsammanin mamakon ruwan da aka tafka ranar Lahadi ne ya rutsa da matashin, inda ya faɗa babban hanyar ruwa kuma ya maƙale.

A wani labarin kuma Wani mutumi na tsaka da murnar nasarar PDP a zaɓe Osun, ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure

Yayin da yake nuna jin daɗinsa da nasarar PDP, wani mutumi ya harbi kansa da bindiga a Ile-Ife ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna cewa an garzaya da shi wani Asibiti mafi kusa kafin daga bisani a maida shi Asibitin koyarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262