Talauci da Jahilci sun yiwa mutane yawa, Shi yasa Suke Sayar da Kuri'u a Najeriya
- Wani jigo a jam’iyyar APC na jihar Anambra ya dora alhakin talauci da jahilci a matsayin dalilin da yasa ake sayar da kuri'u a Najeriya
- Okelekwe ya ce mutane ba sa la’akari da irin wahalhalun da za su sha nan da shekaru hudu, sun gwammace su sayar da kuri'ar su wajen zaben gurbataccen shugaba
- Yazama dole kafafen yada labarai su wayar da kan jama'a akan illar sayar da kuri'un su inji Okelekwe
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Anambara - Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Anambra, , ya dora alhakin talauci da jahilci a matsayin dalilin da ya sa sayen kuri’u a lokacin zabe ke bunkasa a Najeriya. Rahoton PUNCH
Okelekwe, dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar APC a shiyyar Anambra ta tsakiya, ya bayyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar.
Ya koka da cewa, saboda talauci da jahilci, mutane ba sa la’akari da irin wahalhalun da za su sha nan da shekaru hudu, sun gwammace su karbi kudin da bai taka kara ya karya ba kafin su kada kuri’unsu.
Ya ce,
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Siyan kuri’u shine babban kalubalen da ya shafi harkar zabe a yanzu, amma mun san cewa wata rana zai wuce lokaci ne.
Kafin yanzu, a da sace akwatin zabe ake yi, amma sabbin fasahohin da aka yi a harkar zabe sun kawar da hakan.
“Talauci da jahilci ya sa sayen kuri’u yayi muni. Mutum ba zai yi la'akari da ingantaccen ilimi, kiwon lafiya da sauran ribar da za a samu daga shugabanci nagari ba, ya gwammace ya karbi kudi ya kada kuri'a."
"Shiyasa muke bukatar kafafen yada labarai su wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da sayar da kuri’unsu. Duk kuri’ar da ka sayar, ka taimaka wajen dora gurbataccen shugaba.
Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu, Shettima ya fadawa Buhari
A wani labari kuma, Kashim Shettima ya fadawa shugaba Buhari cewa Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu kamar yadda PREMIUM TIMES ta rawaito.
Shettima ya nemi shugaba Buhari ya yiwa Zulum godiya akan yadda ya rika ambaton sunan sa, a duk lokacin da aka masa tayin zama abokin takarar Tinubu.
Asali: Legit.ng