Hadimin gwamnan jihar Nasarawa ya rasu a wani hatsarin mota
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi rashin ɗaya daga cikin hadimansa a wani hatsarin mota
- Mai taimaka wa gwamnan Nasarawa a ɓangaren wutar lantarki, Jamilu Yakubu, ya rasu kuma tuni a ka yi jana'izarsa
- Gwamna Sule ya samu halartar jana'iza kuma ya yi wa baki ɗaya iyalan marigayin ta'aziyya da Addu'a
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Nasarawa - Mai taimakawa gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa kan harkokin wutar lantarki, Jamilu Mohammed Yakubu, ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Yakubu ya rasu ne ranar Talata a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Akwanga-Lafia jihar Nasarawa.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamna, Ibrahim Addra, ya fitar kuma aka raba wa manema labarai kwafi ranar Laraba.
Ya ce mamacin ya taka rawar a zo a gani wajen gina tashar wutar lantar ki (330KV) a Ƙurba da sauran ayyukan samar da wuta a sassan jihar Nasarawa, rahoton dailytrust ya tabbatar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya halarci Jana'iza
Addra yace gwamna Sule ya halarci Jana'izar mamacin hadimin nasa, kuma ya yi wa matarsa, 'ya'ya da kuma baki ɗaya iyalan mamacin ta'aziyya tare da Addu'ar Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.
Gwamnan ya bayyana marigayin da, "Matashin mutum me aiki tuƙuru kuma wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa al-ummar jiharsa aiki."
A cewar Sanarwan, gwamna Sule ya ƙara da cewa:
"Babu tantama rasuwarsa babban rashi ne ba ga iyalansa kaɗai ba har da jihar Nasarawa baki ɗaya duba da ɗumbin gudummuwar da ya bayar wajen cigaban jiha musamman a ɓangaren wutar lantarki."
A wani labarin kuma kun ji cewa wata Jarumar Fina-finai ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu kafin zuwa Asibiti
Fitacciyar jaruma a masana'antar Nollywood, Ada Ameh, ta mutu jim kaɗan bayan ta yanke jiki ta faɗi ba zato a jihar Delta.
Ameh, wacce ta ce ga garinku nan a kan hanyar zuwa Asibiti, ta yi fice a shiri mai dogon zango 'The Johnson' a zamanin rayuwarta.
Asali: Legit.ng