Yan ta'addan ISWAP sun saki sabon bidiyon yadda suka yi babbar Sallah, sun yi barazanar kai hare-hare

Yan ta'addan ISWAP sun saki sabon bidiyon yadda suka yi babbar Sallah, sun yi barazanar kai hare-hare

  • Ƙungiyar ISWAP ta saki wani sabon Bidiyo na yadda mambobinta suka gudanar da bikin babbar Sallah da ta gabata
  • Ƙungiyar wacce ta yi ikirarin kai hari gidan Yarin Kuje, ta yi barazanar kai hare-hare gidajen Yarin Najeriya
  • A watan da ya gabata ne wasu yan ta'adda suka farmaki gidan Yarin Kuje, suka kwance mayaƙan Boko Haram da ke tsare

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Ƙungiyar ta'addanci ISWAP ta saki wani sabon bidiyo da ya nuna mambobinta na shagalin babbar Sallah Eid-el-Kabir da ta wuce kwanan nan a wurare daban-daban.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana tsammanin wuraren da yan ta'addan suka yi shagalin baya wuce gaɓar Tafkin Chadi da kuma wasu ƙauyuka da ke hannun su a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa yayin da Sallah ta gabato, ƙungiyar ta yi shirin gudanar da bikin Babbar Sallah a maɓoyar mayaƙanta kuma ta naɗa Limaman da zasu jagoranci Sallah a wurare daban-daban.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai kazamin hari jihar Katsina da tsakar rana, sun aikata mummunar ɓarna

Yan ta'adda.
Yan ta'addan ISWAP sun saki sabon bidiyon yadda suka yi babbar Sallah, sun yi barazanar kai hare-hare Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A sabon bidiyon wanda ba'a iya tantance fuskokin mutane, ISWAP ta nuna yadda mutane da ƙananan yara suka gudanar da Sallar idi kuma suka yi wasu abubuwa da ya haɗa da Layya kamar yadda Babbar Sallah ta tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata waƙa cikin harshen Hausa da ta biyo bayan huɗubar Liman, tawagar mawaƙan sun haɗa baki suna rera, "Mu haɗa ƙarfi mu kawar da kafirai masu bautar Allolin ƙarya. Yau muna farin ciki da godiyar Allah da zuwan babbar Sallah."

Bayan rera wasu baitocin waƙar wani ɗan ta'adda daga cikinsu yayi jawabi cikin harshen Hausa, inda ya tabbatar wa mayaƙan ƙungiyar dake tsare hannun gwamnati cewa suna nan zuwa kuɓutar da su.

Zamu maimaita harin Kuje

Ya kuma nuna farin cikinsa bisa nasarar ƙungiyarsu na fasa magarƙama, inda suka kubutar da mayaƙansu da ke tsare a gidan Yarin Kuje a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jiha, yan sanda sun ce ba zata saɓu ba

Ya ce:

"Mun gode Allah wanda da ikonsa muke murnar Sallan layya, ya zame mana murna kan murna, murnar sallah da kuma ceto yan uwan mu daga Kuje, wanda ba ƙaramar Rahamar Allah bace ga bayinsa, mun gode masa."
"Saƙon mu ga yan uwa da ke tsare, bamu mance da ku ba kuma ba zamu taɓa mancewa ba matuƙar muna raye. Ya kamata ku sani cewa akwai maimaicin abinda ya faru a Kuje, zaku ji masu jihadi suna Kabbara zasu ceto ku daga hannun maƙiya."
"Muna sanarwa baki ɗaya al'ummar musulmai na duniya da yan uwanmu masu jihadi a ko ina suke cewa Allah da ikonsa ya raya mu har muka sallaci Babbar Sallah kuma muka yi murna cikin kwanciyar hankali."

Bidiyon ya nuna wani mutumi ya na raba abinci da abun sha da wasu kyaututtuka don ta ya murna da farin ciki.

A wani labarin kuma kun ji cewa 'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

Kara karanta wannan

An fara shari'ar Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida mai karfi a Kotu

Yan bindiga sun kutsa kai har cikin gidan wani basarake a Abuja, sun yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da har yanzun ba'a gano ba.

Wani shugaban al'umma a yankin da abun ya faru ya ce maharan sun shafe kusan awa ɗaya amma babu wanda ya kawo ɗauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262