Bidiyon yara 3 da aka tsinta suna gararamba a titin Edo wurin karfe 11 na dare

Bidiyon yara 3 da aka tsinta suna gararamba a titin Edo wurin karfe 11 na dare

  • An tsinta wasu yara kanana uku suna gararamba a lungu da sakon garin Benin City na jihar Edo cikin dare
  • Yaran masu shekaru shida, hudu da biyu sun kai wurin karfe 11 na dare a kusa da kasuwar Santana dake titin Sapele
  • Tuni aka garzaya da yaran ofishin 'yan sanda inda aka tsare su ana kuma cigaba da cigiyar neman wadanda suka san su

An tsinta yara kanana uku suna yawo a lungu da sako na Benin City a jihar Edo a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli wurin karfe 11 na dare.

An tsinta kananan yaran har uku ne a wurin kasuwar Santana dake kan titin Sapele.

Kananan Yara
Bidiyon yara 3 da aka tsinta suna gararamba a titin Edo wurin kafe 11 na dare. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Yaran da aka bayyana sunayensu da Kosisochukwu mai shekaru 6, Chikamso mai shekaru 4 da Chidubem mai shekaru biyu duk an kwashe su zuwa ofishin 'yan sandan jihar Edo inda aka adana su.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga Bayan Musayar Wuta, Sun Kwato Bindigun AK-47 Da Babura

Ga bidiyon yaran a ofishin 'yan sandan:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Dan uwan ango ya bindige amarya ana tsaka da shagalin biki, ta sheka lahira

A wani labari na daban, ana tsaka da shagalin biki, an bindige amarya yayin da 'dan biki ya harba bindiga duk a cikin murna kuma ya sameta a kan ta.

Mahvash Leghaei mai shekaru 24 tayi aure a Firuzabad a Iran yayin da 'dan biki wanda ya kasance 'dan uwan ango ne, ya harba bindigarsa mara lasisi wacce yake amfani da ita wurin farauta.

An gano cewa, kai tsaye harsashin ya shiga kan mata kuma ya jigata 'yan biki maza har su biyu.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Kanal Mehdi Jokar yace: "An yi mana kiran gaggawa kan harbin da aka yi a wurin shagalin biki a birnin Firuzabada kuma a take muka aika jami'ai."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: