Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin Dana Air ya yi saukar gaggawa a Abuja kan wata matsala

Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin Dana Air ya yi saukar gaggawa a Abuja kan wata matsala

  • Jirgin sama na Kamfanin Dana Air ya yi wata saukar gaggawa a babban birnin tarayya Abuja bayan gano injinsa ya samu matsala
  • Wata sanarwa da Kamfanin ya fitar a shafinsa na Tuwita ya ce Fasinjoji 100 da ya ɗakkon sun fita lafiya
  • A halin yanzun Injiniyoyin Kamfanin sun maida hankali wajen shawo kan matsalar

Abuja - Jirgin sama na kamfanin sufurin jiragen sama Dana Air mai lambar rijista (5N DNA) ya yi wata saukar gaggawa a filin jirgin Nnamdi Azikwe biyo bayan wata matsala da ta auku a ɗaya daga cikin injinansa.

Kamfanin sufurin ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Tuwita.

Jirgin Saman Dana Air.
Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin Dana Air ya yi saukar gaggawa a Abuja kan wata matsala Hoto: channelstv
Asali: UGC

A sanarwan da Kamfanin ya fitar ya nuna cewa Jirgin ya yi saukar gaggawa ne da misalin ƙarfe 2:52 na rana kuma babu wanda ya samu rauni daga cikin Fasinjojin jirgin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Sanarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jirgin mu Boeing 737 da ya nufi Abuja mai lambar rijista 5N DNA ya yi saukar gaggawa yau 19 ga watan Yuli, 2022 saboda wasu alamu da ɗaya daga cikin injinansa ya nuna."
"Matuƙin Jirgin ya sanar da Fasinjoji ciki halin da ake ciki kuma ya saukar da Jirgin lami lafiya a filin jirgin sama na ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:52 na rana."
"Baki ɗaya fasinjoji 100 da ke ciki sun fita cikin koshin lafiya yayin da tawagar Injiniyoyin mu suka hau kan jirgin don gyara matsalar. Mun sanar da hukumar sufurin jiragen sama NCAA abinda ya faru."

Wannan ba shi ne na farko ba

Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan hatsari ya rutsa da ɗaya daga cikin jirgaen kamfanin Dana Air a filin jirgin sama na Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

Jirgin mai lamba 5N JOY ya kammala shirye-shiryen tashi daga Patakwal zuwa Legas a ranar 2 ga watan Mayu lokacin da tayoyinsa suka kama da wuta, bisa tilas aka fasa tafiyar.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jiha, sun nemi miliyoyi kudin fansa

Masu garkuwa da mutane ɗauke da makamai sun yi awon gaba da shugaban APC na gunduma ta 9, ƙaramar hukumar Orhionmwon, jihar Edo.

Wata majiya daga cikin iyalan ɗan siyasa, ya bayyana cewa sun nemi a haɗa musu miliyan N5m a matsayin fansa kafin su sako shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262