Tirkashi: Matar aure ta dafa kwai a gaban mota sakamakon tsabar zafin da ake a Turai

Tirkashi: Matar aure ta dafa kwai a gaban mota sakamakon tsabar zafin da ake a Turai

  • Wata mata mai suna Jill ta bayyana yadda ta dafa kwai a gaban motar ta kirar Honda sakamakon tsabar zafin da ya addabi Turai
  • Ba Jill kadai ba, Gladys mazauniyar Turai ta sanar da yadda ta soya kwai kacokan a gaban motar ta sakamakon zafin motar ta ya kai
  • Jama'a mazauan Turai suna kokawa kan zafin da ke kaiwa 45 zuwa 58 na ma'aunin Celsius a fadin yankunan

Jill ta yi amfani da na'urar gwada dumi kuma tayi ikirarin cewa motar ta kirar Honda Civic inda take saka kaskon suyar kwai yana da zafi ma'aunin Celsius 45.

Ta ce: "Ma'aunin zafin ya kai sama sannan ya mutu bayan ta saka shi a saman motar ta."

Boiled Egg
Tirkashi: Matar aure ta dafa kwai a gaban mota sakamakon tsabar zafin da ake a UK. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

LIB ta ruwaito cewa, Jill tace tana son dafa kwai tare da Salmon da biredi. Jill ba ita kadai bace mai dafa kwai a saman motarta.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

Wata mata mai suna Gladys ta wallafa bidiyo a TikTok inda take soya kwai a saman mota kuma zafin motar yana nuna ya kai 40 na ma'aunin Celsius.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gladys tace: "Ina aiki a matsayin mai kula da al'umma kuma muna fuskantar zafi idan muna yawo a mota wanda hakan ya kai ga na siyo ma'auni domin gwadawa. Zafin ya kai 58.3 na ma'aunin Celsius.
"A ranar da muke tattaunawa kan zafin gari da kawata, sai nayi tunanin ko zan iya girka wani abu a mota. Don haka sai na gwada soya kwai. Ya soyu kuma tsaf bayan na yi zaman sa'a daya a motar. Abun akwai mamaki."

Bidiyo: Baturiya da ta aura 'dan Najeriya tace tana jin dadi, ta shiga cikin matan kauye tana shara da wanki

A wani labari na daban, wata baturiya wacce ta auri dan Najeriya ta bayyana yadda take jin dadin zama da mijin ta dan Najeriya. Ta wallafa bidiyon kanta tana ayyukan gida a Najeriya tare da wasu matan kauye.

Kara karanta wannan

Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari

Yayin wallafa bidiyon, tace gaskiya akwai sauki sabo da rayuwar Najeriya saboda tun farko ta saba yin ayyukan gida.

Kamar yadda kyakyawar matar wacce aka yi wa lakabi da sunan mace ta gari, tace tana jin dadin zaman ta a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng