Saura kiris: Muna ta kokarin kawo karshen yajin aikin ASUU, inji gwamnatin Buhari
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana aiki tukuru wajen tabbatar da yajin da aikin da ASUU ke yi zai zo karshe dindindin
- Kungiyar malaman jami'a a Najeriya sun shafe watanni suna yajin aiki bisa rashin biya musu bukatunsu na alawus
- Hakazalika, COASU ma sun shiga yajin aiki, wanda suke jiran kammala tattaunawa da gwamnatin tarayya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Adamawa - Gwamnatin tarayya ta ce ba wai kawai ta na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi a halin yanzu bane, a’a, tana ma kokarin kawar da yajin aikin da kungiyar ke yi ne har zuwa nan gaba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a taron koli karo na 81 na kwamitin ba da shawara kan harkokin ilimi (JCCE) da aka gudanar a Yola jihar Adamawa, The Nation ta ruwaito.
Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo, wanda ya zanta da manema labarai a gefen taron, ya jaddada cewa ana ci gaba da daukar matakai domin bai kamata ace ASUU ta sake yajin aiki a nan gaba ba.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Gwamnati na yin komai domin ganin ‘yan kungiyar ASUU sun dawo bakin aiki.”
Ya kara da cewa:
“A yayin da nake magana, ina tabbatar muku cewa gwamnati ba ta barci kan yaranmu ba sa makaranta. Batutuwan da ake tattaunawa sun hada da cewa idan aka kammala da ASUU ba za ta sake shiga yajin aikin ba."
Da aka nemi jin ta bakinsa kan kungiyar ma’aikatan Kwalejin Ilimi (COASU) wadda ita ma mambobinta ke yajin aiki, Adejo ya ce nan ba da jimawa ba mambobin COASU za su sami damar komawa bakin aiki.
A cewarsa:
"Da alama COASU za ta janye yajin aikin na ta nan ba da dadewa ba saboda ana magance matsalolinsu kuma an yi nisa da tattaunawa.
Taron na kwanaki biyar na 81 na JCCE, wanda aka fara a ranar Litinin, an shirya zai gudana ne har zuwa Juma'a.
Kungiyar NUBIFIE ta bayyana yiwuwar shiga yajin na ASUU domin nuna goyon baya ga fafutukar kungiyar, inji rahoton Guardian.
Yajin aiki: Ma'aikatan jiragen sama zasu rufe filayen jirage don taya ASUU nuna fushi
A wani labarin, kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta shiga yi ko kuma za su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hada kai da malaman jami’o’in.
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba, rahoton Leadership.
ANAP ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi na kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa kyau da ke iya lalata makomarsu.
Asali: Legit.ng