ASUU: Hotunan dalibin da ya bude gidan cin abinci, shi ke girkawa kuma yake siyarwa

ASUU: Hotunan dalibin da ya bude gidan cin abinci, shi ke girkawa kuma yake siyarwa

  • Wani matashin dalibin jami'ar akin noma ta Abeoukuta mai suna Alagbe Emmanuel Adekunle ya bude wurin cin abinci sakamakon yajin aikin ASUU
  • Dalibin ya sanar da Legit.ng cewa ya koyi girki daga wurin mahaifiyarsa amma da kyar iyayensa suka ba shi ya fara sana'ar girkin
  • Ya bayyana cewa, yana da burin bude babban gidan cin abinci amma yana fatan samun jari mai kauri domin tabbatar da cikar burinsa

Legas - Wani matashi dalibin Najeriya ya bayyana yadda rayuwa ta juya masa bayan kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'in Najeriya sun tsunduma yajin aiki.

Ya sanar da cewa, shi alheri wannan yajin aikin ya zame masa saboda ya yi amfani da lokacinsa yadda ya dace.

Emex Chops
ASUU: Hotunan dalibin da ya bude gidan cin abinci, shi ke girkawa kuma yake siyarwa. Hoto daga @olowosibiii
Asali: Twitter

Ya yanke hukuncin yin amfani da zaman gida na dolen ta hanyar siyar da abinci a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa da ta kai kwarto daki, tana kokarin fitar dashi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matashin mai amfani da sunan @olowosibii a Twitter ya bude gidan cin abinci na yanar gizo wanda yake aiki a matsayin mai girkin kuma mai siyarwa.

Ya sanya burin cewa, wannan aikin da yake ba zai tashi a banza ba inda ya wallafa hotunan kansa da kayan kuku tare da wani hoton inda yake shirya girki a madafinsa.

"Ni matashin kuku ne kuma mai yin abincin siyarwa, ina aiki tukuru wurin tabbatar da na kafa kasuwanci na. A matsayinsa na dalibin da yajin aikin ASUU ya shafa, ina da gidan cin abinci na yanar gizo.
"Na yadda cewa, akwai mutunci a aiki tukuru kuma aikin da nake yi ba zai fadi a banza ba," @olowosibiii yace.

Legit.ng Hausa ta zanta da dalibin inda ya bayyana cewa sunansa Alagbe Emmanuel Adekunle, yana aji daya a jami'ar aikin noma dake Abeoukuta, jihar Ogun amma yana zama a Legas.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Fusatattun jama'a sun yi wa matashi tumɓur bayan an kama shi yana satar ɗan kamfan mata

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng