'Yan bindiga sun sace wata mace da tsohon ciki da wasu mutane a Zariya

'Yan bindiga sun sace wata mace da tsohon ciki da wasu mutane a Zariya

  • Wasu yan bindiga sun sake kai hari wani yanki da ke kusa da makarantar sojoji NDA, Mando, a jihar Kaduna
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da mai juna biyu da wasu mutane Bakwai a harin wanda suka shiga gida-gida
  • Kakakin hukumar yan sandan Kaduna ya ce ba shi da masaniya amma zai bincika kafin ya yi magana a kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zaria, jihar Kaduna - Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da wata mai juna biyu a yankin Lema, Mando da ke hannun riga da makarantar sojoji (NDA), a jihar Kaduna.

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da wasu mutum Bakwai bayan matar a harin wanda suka shiga gida-gida da misalin ƙarfe 1:00 na dare yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

Jihar Kaduna.
'Yan bindiga sun sace wata mace da tsohon ciki da wasu mutane a Zariya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin mazaunan yankin, Musa Ɗanladi, ya ce mutane sun ji tsoron fitowa daga gidajen su saboda ƙarar harbin da 'yan bindigan suke yi.

Malam Ɗanladi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun zo da kusan ƙarfe 1:00 na dare kuma suka yi awon gaba da mutane Takwas cikin su har da mai juna biyu wacce aka ce ta zo gaida mahaifiyarta ne da bata da lafiya a yankin."

Sauran mazauna yankin sun nuna damuwarsu tare da yin kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen ceto su daga faruwar irin haka.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun bayan aukuwar lamarin, har yanzun gwamnati ba ta fitar da sanarwa game da harin a hukumance ba.

Haka zalika, da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai bincika abun da ya faru kafin ya yi magana a hukumance.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Sai dai har zuwa lokacin da muke haɗa rahoton nan, kakakin 'yan sandan bai fitar da bayanai kan abinda ya faru ba.

A wani labarin na daban kuma Shugabar mata ta jam'iyyar APC, Kemi Nelson, ta rasu tana da shekaru 66

Shugabar matan jam'iyyar APC reshen shiyyar kudu maso yamma, Kemi Nelson, ta rigamu gidan gaskiya tana da shekara 66.

Bayanai sun nuna cewa Nelson ta rasu ne yau Lahadi bayan fama da jinya, yau a asibiti gobe a gida tun 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262