Shugabar mata ta jam'iyyar APC, Kemi Nelson, ta rasu tana da shekaru 66
- Shugabar matan jam'iyyar APC reshen shiyyar kudu maso yamma, Kemi Nelson, ta rigamu gidan gaskiya tana da shekara 66
- Bayanai sun nuna cewa Nelson ta rasu ne yau Lahadi bayan fama da jinya, yau a asibiti gobe a gida tun 2020
- Kafin rasuwarta ta rike manyan muƙamai kuma ta hannun dama ce a masoyan tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Tsohuwar shugabar asusun inshora ta ƙasa (NSITF) kuma shugabar mata ta shiyya a jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Kemi Nelson, ta riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Nelson ta kwanta dama ne da safiyar nan ta Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022, bayan fama da dogon rashin lafiya.
Bayanai sun nuna cewa ta kasance yau a Asibiti gobe kuma a gida tun bayan lokacin da ta yi murnar cika shekara 64 a duniya a shekarar 2022.
Kafin rasuwarta, Jigon APC ita ce 'Yeye Oge' ta jihar Legas kuma ta hannun ɗama ce a cikin magoya da masoyan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Manyan muƙaman da ta rike
A zamanin rayuwarta, Kemi Nelson, ta rike kwamishina a ma'aikatar harkokin mata da daƙile talauci lokacin mulkin Tinubu yayin da yake kan kujerar gwamnan Legas.
Haka zalika ta yi aiki a matsayin shugabar matan APC reshen jihar Legas kafin daga bisani aka maida ita shugabar matan APC ta shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.
Kemi Nelosn ta kasance mace ɗaya tilo mamba a majalisar shawarin gwamnan jihar Legas da ake kira GAC a taƙaice, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Bugu da ƙari ta rike Daraktan asusun ba da inshora na ƙasa, (NSITF) kuma ta jagoranci ma'aikatar aiwatarwa, horo da kuma samar da ayyukan yi.
Marigayyar ta auri Daraktan ma'aikatar harkokin cikin gida ta tarayya wanda ya yi ritaya, Adeyemi Nelson, a 1987 kuma Allah ya albarkace su da 'ya'ya uku.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya ana dab da zaɓe, wata jam'iyyar adawa ta koma bayan ɗan takararta
Awanni kafin fara kaɗa kuri'a, jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya a jihar Osun.
Jam'iyyar AD wato Alliance for Democracy ta umarci baki ɗaya masoya da magoya baya su dangwalawa gwamna Oyetola a zaɓen gobe.
Asali: Legit.ng