Zaben Osun: Jami'an EFCC Sun Damke A Kalla Mutane 3 Kan Siyar Kuri'un Zabe
- Jami'an hukumar EFCC sun kama wasu mutane a kalla uku da ake zargi da sayan kuri'a a zaben gwamna na Jihar Osun da ake yi yau Asabar
- EFCC ta ce jami'an nata sun cafke wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri da kuma hujjoji ta kafar zamani da ke nuna mutane wai suna cinikayyar kuri'u
- Hukumar ta yaki da rashawar ta ce ba za ta bata lokaci ba za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin a fara shari'a a hukunta su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Osun - Jami'an hukumar yaki da rashawa ta yi wa tattalin arzikin kasa ta'anatti, EFCC, sun kama a kalla mutane uku da ake zargi da sayan kuri'un masu zabe a zaben gwamnan Jihar Osun da ke gudana.
Hukumar yaki da rashawar ta ce a ranar Asabar ta samu bayanai na sirri da kuma ta kafafen zamani, jami'anta sun kama wadanda ake zargin da aka dauki hotuna da bidiyonsu wai suna cinikayyar kuri'un.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An kama wasu daga cikin wadanda ake zargin ne a Gunduma ta 2 Ifelodun Street a Osun Jihar Osogbo, babban birnin Jihar.
Hukumar ta shaidawa Channels TV cewa nan take za ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotu don fara aikin hukunta su.
Ministan Buhari Ya Gujewa Zaben Gwamna a Jiharsa Ya Shilla Jamus
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya gujewa zaben gwamna da ake yi a jihar Osun.
Jaridar Daily Trust tattaro cewa Aregbesola, wanda a halin yanzu ya ke takun saka da tsohon shugaban ma'aikatan fadarsa kuma magajinsa, Gboyega Oyetola, a halin yanzu yana Jamus.
Yan jarida sun tafi akwatin zabensa a Ilesha, suka gano cewa Ministan Harkokin Cikin Gidan ba zai yi zaben ba.
Hadimin ministan a bangaren watsa labarai, Jane Osuji, ta tabbatarwa Daily Trust cewa Aregbesola a halin yanzu baya kasar.
Asali: Legit.ng