Yan sanda sun kama wani Fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje a Katsina

Yan sanda sun kama wani Fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje a Katsina

  • Wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje yayin harin yan ta'adda ya shiga hannu a jihar Katsina
  • Yan sanda sun yi ram da Kamala Abubakar a wata maboyar masu aikata laifuka dauke da wasu kayan laifi a yankin Ɗanmusa
  • Yan ta'adda da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari Kuje, inda suka kwance yan ta'addan da ake tsare da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Hukumar yan sanda reshen jihar Katsina ta yi ram da wani mai suna Kamala Lawal Abubakar, mazaunin Unguwar Sale, karamar hukumar Ɗanmusa, ɗaya ɗaga cikin Fursunonin da suka tsere daga gidan Yarin Kuje, Abuja.

Da yake gabatar da wanda ake zargi, kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, ya ce mutumin ya shiga hannu ne a wani wuri da ake zargin maɓoyar masu aikata mugggan laifuka ne a Ɗanmusa.

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun

Fursunan Kuje ya shiga hannu a Katsina
Yan sanda sun kama wani Fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje a Katsina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A rahoton da jaridar Daily Trust ta tattara, Isa ya ce bayan sun samu wasu bayanan sirri, nan take dakaru suka dira wurin kuma suka yi nasarar kama wanda ake zargi.

SP Gambo Isa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yayin gudanar da bincike wanda ake zargin ya amsa cewa ya gudo ne daga gidan yarin Kuje, Abuja lokacin da yan ta'adda suka kai hari a baya-bayan nan."
"An samu busassun ganyayyaki da ake zargin tabar wiwi ce a tare da shi yayin da yan sanda suka tsananta bincike. Zamu miƙa shi hannun jami'an gyaran hali domin ɗaukar mataki na gaba."

Bugu da ƙari, Kakakin ya ƙara da cewa hukumar yan sanda ta kammala shirye-shiryen miƙa shi hannun Jami'an gyaran hali da ke aiki a gidajen Yari domin sake garƙame shi a Kuje.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyoyin Naira na fansar Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka rage

Dakaru sun kama kasurgumin mai garkuwa

Sauran waɗan da ake zargi da hukumar yan sanda ta gabatar ya haɗa da wani Bello Sale Jino, ɗan shekara 25 ɗan yankin Medoji da ke cikin birnin Katsina, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ana zargin Bello Sale da jagorantar tawagar masu garkuwa da mutane da kuma yan ta'adda da suka hana zaman lafiya a wasu sassan jihar Katsina.

A wani labarin kuma Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

Jaruman yan sanda a Jihar Nasarawa sunyi nasarar kama daya cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja.

An kama, wanda ake zargi dan Boko Haram ne, Hassan Hassan a karamar hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa yana kokarin tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262