Gwamna Zulum Ya Bawa Yan Sanda Gidaje 259 da kudi N110m A Borno
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya baiwa Yansanda Gidaje 259 da kyautar N110m A Borno
- Rundunar Yansandan Najeriya ta kaddamar da bankin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank)
- Gwamana Babagana Umara Zulum ya yabawa IGP Alkali bisa kaddamar da reshen bankin na Borno
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis a Maiduguri, ya bayyana cewa gwamnati ta ware gidaje 259 tare da sakin N110m ga rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar. Rahoton INDEPENDENT
Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bankin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank).
An tsara bankin Microfinance ne don samar da ayyukan kudi don tallafa wa kanana da matsakaitan sana’o’i ga iyalan ‘yan sanda, abokan hulda da fararen hula a jihar Borno.
Bude bankin a Maiduguri ya samu halartar babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kafin kaddamar da taron, Zulum ya bayyana cewa rabon gidaje sama da 259 ga ‘yan sanda an yi shi ne domin biyan diyya ga rundunar jihar kan yadda gwamnati ta yi amfani da wasu filaye mallakar ‘yan sanda da kuma bunkasa wasu kayayyakin more rayuwa a babban birnin jihar.
Zulum ya yabawa IGP Alkali bisa kaddamar da reshen bankin na Borno wanda ya ce, ya nuna yadda IGP ya ba da fifiko ga jin dadin ‘yan sanda.
Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar 'Buhari Must Go'
A wani labari, Jihar Kogi - Wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kogi, a ranar Alhamis, ta saki wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama guda biyu, da jihar yiwa hukunci saboda sun lika allunan zanga-zanga mai taken ‘Buhari must Go’ a watan Afrilun 2021. Rahoton Jaridar PUNCH Alkalin kotun
Mai shari’a Tanko Muhammed ya yi watsi da karar Amini Udoka da Emmanuel Larry mai lamba: CMCL/123m/2021 bayan an dage sauraron karar.
Asali: Legit.ng