Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar 'Buhari Must Go'
- Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar neman shugaba Buhari ya sauka daga karagar mulki a jihar Kogi
- Matasan da suka gudanar da zanga-zangar 'Buhari Must Go' sunce za su shigar da kara akan cin zarafin su da akayi
- Rahotanni sun nuna matasan da ake zargi sun ci mutuncin shugabankasa Muhammadu Buhari sun shafe kwanaki 78 a tsare kafin aka ba da belin su
Jihar Kogi - Wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kogi, a ranar Alhamis, ta saki wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama guda biyu, da jihar yiwa hukunci saboda sun lika allunan zanga-zanga mai taken ‘Buhari must Go’ a watan Afrilun 2021. Rahoton Jaridar PUNCH
Alkalin kotun Mai shari’a Tanko Muhammed ya yi watsi da karar Amini Udoka da Emmanuel Larry mai lamba: CMCL/123m/2021 bayan an dage sauraron karar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Edeh, ya ce an kama mutanen biyu ne a ranar 5 ga Afrilu, 2021, bisa zargin cin mutuncin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a Lokoja, babban birnin jihar.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan daba sun yi masu duka kuma sun shafe kwanaki 78 a tsare kafin aka ba da belinsu a bara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake magana da wakilan jaridar PUNCH, daya daga cikin wadanda ake tuhumar, Udoka, ya ce:
“Wannan shi ne nasarar mu na farko ,kuma za mu shigar da kara akan cin zarafin mu da aka yi.”
Ya kara da cewa lamarin yasa ya shiga cikin dimuwa, kuma yana fama da matsalar rashin lafiya sakamakon tsare shi da aka yi.
Tinubu ya birkita lissafin Gwamnonin Arewa da ya dauko Shettima – Hadimin Buhari
A wani labari kuma kunji cewa, Abuja - Yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya sun ji haushin rasa tikitin mataimakin shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki.
Ismael Ahmed ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022, inda ya yi sharhi a game da takarar shugaban kasa a APC
Asali: Legit.ng