FG ta fitar da jerin sunayen wasu daraktoci 14 don zabar Akanta Janar a cikinsu
- Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara shirye-shiryen nada sabon Akanta Janar na tarayya
- A ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ne Mariya Rufai, daraktar gudanarwa ta ofishin Akanta Janar ta fitar da takarda dauke da sunayen daraktoci 14 don darewa kujerar
- Kujerar dai ya zama a kasuwa ne tun bayan da aka dakatar da tsohon AGF, Ahmed Idris, kan zarginsa da ake da aikata rashawa
Abuja - An fara shirye-shiryen nada sabon Akanta Janar na tarayya yayin da gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wasu daraktoci 14 da ke mataki na 17 a aikin gwamnati a ranar Laraba,13 ga watan Yuli.
Kujerar ya zama babu kowa bayan dakatar da tsohon AGF, Ahmed Idris da aka yi kan zargin wawure kudi naira biliyan 80.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun Mariya Rufai, daraktar gudanarwa ta ofishin Akanta Janar na tarayya, wanda shugabar ma’aikatan gwamnati, Dr Folasade Yemi-Esan ta karba, jaridar Vanguard ta rahoto.
The Nation ta rahoto cewa sunayen wadanda aka fitar sune: Muhammad Murtala Saleh, Chizea Onochie Peter da Lydia Jafiya Shehu dukkaninsu daga ofishin AGF.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sauran sune Bakre Modupe Julianah (ma’aikatar harkokin yan sanda), Ibrahim Saadiya Jibo, Omachi Raymond Omenka (Ma’aikatar cikin gida), Danladi Comfort Zakiwi (NSCDC) da Abah George Fidelis (hukumar kula da shige da fice na Najeriya).
Sai kuma Mohammed Aminu YarAbba (hukumar kashe gobara ta tarayya), Samuel Waziri (ma’aikatar noma da raya karkara), Mahmud Adam Kambari (hukumar ci gaban Arewa maso gabas), Mohammed Magaji Doho (ma’aikatar ilimi), Mufutahu Bukolah (ma’aikatar sufuri), da Yusuf Abdullahi Musa (ma’aikatar labarai da al’adu).
A kwanan nan ne aka tsige Chukwuyere Anamekwe wanda ke rikon kwarya sannan aka maye gurbinsa da tsohon daraktan asusun bai daya wato TSA, Okolieaboh Ezekiel Sylvis.
Da dama sun alakanta tsige Anamekwe da cewa da ya yi gwamnatin tarayya na cin bashi ne don biyan albashi.
Rashawa: Ba a gama da AGF da ya saci biliyoyi ba, an maye gurbin wanda aka nada a kujerarsa
Mun dai ji a baya cewa gwamnatin tarayya ta maye gurbin Mista Chukwuyere N. Anamekwe a matsayin mukaddashin Akanta Janar na tarayya (AGF), kamar yadda rahotanni suka bayyana a karshen mako.
An maye gurbinsa ne makonni biyu da suka gabata da wani, AGF Mista Okolieaboh Ezeoke Sylvis, tsohon Daraktan TSA (Asusun bai daya na tarayya).
The Nation ta gano cewa maye gurbin Anamekwe ya biyo bayan zargin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke bincikensa akai.
Asali: Legit.ng