Bayan Musuluntar mijinta, matar aure ta bi sahu, tace kyawawan dabi'un da ya koma ne suka ja ta

Bayan Musuluntar mijinta, matar aure ta bi sahu, tace kyawawan dabi'un da ya koma ne suka ja ta

  • Wata matar aure mai suna Chinonso ta koma Amina bayan ta karba kalmar shahada a garin Owerri dake jihar Imo
  • Matar auren ta bayyana cewa, sauyawar halayen mijinta zuwa kyawawa bayan ya koma Musulunci suka sa ta bi sahun shi ita ma
  • A cewar Aisha Obi, matar auren da farko ta fusata bayan mijinta ya Musulunta, amma ganin canjinsa da kuma jin lamurran addini yasa ta bi sahu

Imo - Aishat Obi, wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta ta Facebook 'ya asalin jihar Imo mai zama a birnin Owerri, ta bayyana yadda wata matar aure ta Musulunta.

Ba shiga Musuluncin matar auren bane abun mamaki, yadda kyawawan halayen mijinta da ya Musulunta ne suka janyota addinin ya birge jama'a.

Aishat Obi and Amina
Bayan Musuluntar mijinta, matar aure ta bi sahu, tace kyawawan dabi'un da ya koma ne suka ja ta. Hoto daga Aishat Obi
Asali: Facebook

Kamar yadda Aishat Obi ta wallafar a shafinta na Facebook, ta sanar da cewa matar auren mai suna Chinonso ta zo ta sameta cike da fushi tana bata labarin yadda mijinta ya musulunta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata a baya

Amma bayan ta bata kalamai tare da tausarta, matar auren ta karba kalmar shahada bayan wata biyu sakamakon yadda halayen mijinta suka sauya sannan ta ji wasu al'amuan addinin Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda tace:

"Amincin Allah ya tabbata a gare ku 'yan uwana maza da mata a Musulunci. Don Allah ku taya ni maraba da 'yar uwa Chinonso wacce a yanzu ta koma Aminat a Musulunci.
"Ta zo wurina tana son ta fahimci abinda mijinta yake yi da Hausawa a cocinsu (masallaci) na tsawon wata biyu.
"Da farko ta fusata sosai kan cewa mijinta ya fara sallah kamar yadda Hausawa suke yi. Amma kuma sai dabi'unsa suka canza zuwa kyawawa.
"Bayan ta ji wasu bayanai game da kyawun Musulunci, ta yanke shawarar zama Musulma. Godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya bani karfin guiwar jure fushinta tare da kwantar mata da hankali.

Kara karanta wannan

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

"Ina rokon 'yan uwana maza da mata dake kira zuwa ga addinin Allah da su kasance masu hakuri da halayyar mutane a koda yaushe. Ina fatan Allah ya saukake mana dukkanmu."

Idan da mai bukata, a neme ni: Bidiyon dirarriyar BaAmurkiya da tace 'dan Najeriya take son aure

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar kasar Amurka ta bayyana bukatarta fili ta son aure namiji 'dan Najeriya. Budurwar da ke bukatar mijin, an ganta a wani bidiyo da ma'abocin amfani da Facebook, Bala Baba Dihis ya wallafa.

Kamar yadda tsokacinsa ya bayyana, budurwar ta bayyana mazaunanta a karshen bidiyon domin jan hankalin mazan.

Da murmushi a fuskarta, budurwar tace tana neman namiji 'dan Najeriya da ke son komawa Amurka kuma su karashe rayuwarsu tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng