Wankan sallah: Hadadden hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza

Wankan sallah: Hadadden hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza

  • Allah ya azurta gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da haihuwar yara da yawa kuma yawancinsu maza ne
  • A wani hoto da ya bayyana a yanar gizo, an gano gwamnan tsaye a tsakanin yaransa maza yayin da suka dau wankan sallah
  • Matawalle ya yi anko iri daya da yaran nasa na farar shadda dinkin babbar riga inda kawunansu ke dauke da hulunan zanna bukar

Wani hoto da ba a saba gani ba na gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle cikin iyalinsa ya bayyana a shafukan sadarwa.

A cikin hoton, an gano gwamnan a tsakanin kyawawan yaransa maza inda kowannensu ke sanye da tufafi iri guda na farar shadda dinkin babban riga.

Gwamna Bello Matawalle da yaransa maza
Wankan sallah: Hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Kamar yadda shafin LIB ya wallafa, Bello Mtawalle na da matan aure guda hudu wadanda suka hada da Aisha, Balkisu, Fatima da Dadiya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda ake rayuwa a cikin gidan gurgu magidanci mai mata 17 da 'ya'ya 84

Haka kuma Allah ya azu ya wallafa, Bello Matawalle na da matan aure guda hudu wadanda suka hada da Aisha, Balkisu, Fatima da Dadiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Magidanci yayi shagalin sallarsa da matansa 3 da 'ya'ya 19, hotunansu sun janyo cece-kuce

A wani labarin, wani 'dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da 'ya'yansa 19.

Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.

A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da 'ya'yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng