Bidiyo: Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata a baya
- Wata matar aure mai amfani da @abdulshally a shafinta na Instagram ta bayyana yadda ta bai wa mai kayan miya kyautar N1 miliyan a Sokoto bayan kwashe shekaru basu hadu ba
- Tace mahaifiyarta na aikenta karbo bashin kayan miya kuma yana basu ba tare da ya matsa a bashi kudinsa ba, har ya hada da biskit da alawa ya bata lokacin tana yarinya
- Ta bashi kyautar ne domin ya kara jari sannan ta nuna godiya kan karamcin da yayi musu, lamarin da yasa shi zubda hawaye saboda farin ciki
Wata matar aure mai amfani da suna @abdulshally ta bai wa mutane mamaki da irin karamcinta tare da tuna alherinta.
Matar auren ta bayyana yadda ta nemi wani tsoho mai suna Shehule mai kayan miya inda ta gwangwaje shi da kyautar N1 miliyan saboda kyautatawa mahaifiyar ta da yayi a lokacin tana karama.
Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki
Kamar yadda ta labarta, sai da ta kwashe sa'o'i uku tana neman Shehule a Arkilla dake jihar Sokoto. A cewarta, yana da shagon langa-langa kuma a nan yake siyar da kayan miya, kayan dandano da kuma kayan ciye-ciyen yara.
"Na je neman wannan mutumin kirkin a yankin tsohon gidanmu, sai da na kwashe sa'o'i uku ina nemansu. Sunan shi Shehule, idan kana zama ko ka taba zama a Arkilla, Sokoto, tabbas zaka san wannan mutumin. Yana da shagon langa-langa inda yake siyar da kayan miya, kayan dandano da kuma kayan kwalam na yara."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mutum ne mai kirki, mahaifiyata tana aikena in karba mata kaya bashi kuma sai ya bani da yawa. A wasu lokuta, idan na siya ganye, zai kara min da tumatur, kayan yaji da albasa kuma duk kyauta. Yana bani biskit da alawa duk lokacin da naje shagon. Wadannan kananan karamcin yasa ni farin ciki a lokacin ina yarinya.
"Da ya ganni ya dinga zubda hawaye, ba wai saboda farin ciki kadai ba, ya kasance yadda na tuna da shi kuma naje nemansa. Har yanzu yana siyar da kayan miya amma a wuri daban. Na bashi miliyan daya ya kara jari. Na fada mishi, bana manta mutane ballantana wadanda suka kasance masu tausasawa gareni da 'yan uwana."
Ta kara da yin bayanin cewa:
"Bana manta mutane iri uku a rayuwata. Wadanda suka taimakeni lokacin ina cikin tsanani, wadanda suka bar ni lokacin ina cikin tsanani da wadanda suka saka ni a mawuyacin hali."
Asali: Legit.ng