'Yan fashi: Matawalle ya bukaci da a tsawaita shekarun ritaya na jami'an tsaro zuwa 70
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya Bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin ritayar jami’an tsaro a Najeriya zuwa shekaru 70
- Matawalle ya ce tsawaita shekarun jami'an tsaro zai taimaka wajen dorewar nasarorin tsaro da aka samu a yaki da ta'adanci
- Gwamnan jihar Zamfara yayi ikrarin mayar da jihar Zamfara jiha mafi zaman lafiya a fadin Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin ritayar jami’an tsaro a Najeriya zuwa shekaru 70, inda ya kara da cewa ya kamata a tsawaita shekarun shiga aikin Short Service daga shekaru 30 zuwa 32 domin samun karin ma’aikata. Rahoton jaridar PUNCH
Sai kuma a ba wa maza da mata masu karfi jiki dake son shiga aikin jami’an tsaro damar yi wa kasar su hidima don tabbatar da tsaro a Najeriya.
Gwamna Matawalle wanda ya yi jawabi a gidan sa da ke Maradun, ya ce hakan zai sa wadanda ba su gajiyawa su ci gaba da yi wa kasa hidima.
Ya ce hakan zai taimaka wajen dorewar nasarorin da aka samu a yaki da ta'addanci da rashin tsaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matawalle ya kuma yi alkawarin mayar da Zamfara jiha mafi zaman lafiya a Najeriya.
Dangane da rashin tsaro da jihar ke fuskanta, gwamnan ya ce;
“Kamar yadda kuka sani muna fuskantar matsalar rashin tsaro a Zamfara. Ina so in mayar da Zamfara jiha mafi zaman lafiya a Najeriya. Ina so in tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.” Rahotom jaridar LEADERSHIP
Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume
Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar. Rahoton Premium Times
Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.
Asali: Legit.ng