Da Dumi-Dumi: Akwai matuƙar wahala, na ƙosa na kammala wa'adina, Buhari ya koka
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ba ƙaramar wahala ya ke sha ba domin ya kosa wa'adin mulkinsa ya ƙare ya koma Daura
- Da yake jawabi ga gwamnonin APC da wasu shugabannin siyasa, Buhari ya ce ya gode Allah mutane sun yaba da ƙoƙarinsa
- Game da rashin tsaro, shugaban ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori a wasu sassan Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Daura, jihar Katsina - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya ƙosa ya miƙa wa magajinsa mulkin Najeriya saboda, "ya sha matukar wuya." kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ƙasan ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jam'iyyar APC, yan majalisu da jagororin siyasa a gidansa da ke garin Daura, jihar Katsina, ranar Litinin.
Buhari ya bar fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja zuwa mahaifarsa wato Daura a ranar Jumu'a domin gudanar da shagulgulan babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a gida.
Shugaban ƙasan ya gargaɗi baƙinsa cewa su yi takatsantsan wajen taimaka wa mafi yawan 'yan Najeriya da ke neman samun wasu damarmaki don su dama.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa, Buhari ya ce:
"A irin wannan lokacin na shekara mai zuwa na cimma ƙarshen zangon mulki na guda biyu kuma sauran 'yan watannin da suka rage, zan yi iya kacin bakin kokari na."
Buhari ya shaida wa gwamnoni da kuma jagororin siyasa cewa rabonsa na zuwa gidansa na Daura kusan shekara ɗaya kenan kuma ba don komai ba sai don aikin Ofis.
Ya ƙara da cewa da zaran ya gama wa'adin mulkinsa zai koma gidansa na Daura da zama ba wai Kaduna ba inda ya ke da babban gida.
"Ina wa duk mutumin da zai karɓi Najeriya bayan na gama fatan nagari," inji shugaban ƙasa.
Ina aka kwana game da matsalar tsaro a Najeriya?
Game da matsalolin tsaro, Shugaban ƙasa ya ce arewa maso yamma ne ke fama da kalubalen rashin tsaro, amma gwamnatinsa ta samu nasara sosai a sauran sassan ƙasar nan kamar arewa maso gabas da kudu maso kudanci.
"Na ƙagara na tafi, zan iya faɗa muku cewa na sha wahala. Ina gode wa Allah saboda mutane suna yaba wa da sadaukarwar da muke yi."
A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnonin APC 9 a Daura
Gwamnonin cigaba na jam'iyyar APC guda Tara sun kai ziyarar barka da Sallah ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.
Bayan ganawar sirri da Buhari, gwamnonin sun bayyana cewa Tinubu da Shettima za su kara haskaka cigaban APC.
Asali: Legit.ng