Kyawawan hotunan Ango AGF Malami da amaryarsa Nana Hadiza Buhari sun bayyana
- Kyawawan hotunan sabon ango AGF Abubakar Malami, da dalleliyar amaryarsa, Nana Hadiza sun bayyana
- A ranar Juma'a, 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Malami da Hadiza a wani kebantaccen biki a Abuja
- Kyakyawar amarya Nana Hadiza Buhari ita ce ta uku a gidan Malami bayan uwargida Aisha da ta tsakiya Fatima
Antoni janar na tarayya, AGF Abubakar Malami ya auri diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Nana Hadiza Buhari a ranar Juma'a, 8 ga watan Yulin 2022.
Nana Hadiza mai shekaru 41 ita ce diyar shugaban kasan ta uku da marigayiyar tsohuwar matarsa, Safinatu.
Nana Hadiza ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi wanda suka haifa 'ya'ya shida da shi kafin rabuwar aurensu.
A halin yanzu, Nana Hadiza ita ce mace ta uku a gidan Malami bayan Aisha uwargida da Fatima ta tsakiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kyawawan hotunan amarya Hadiza da Ango Abubakar Malami sun bayyana kuma sun matukar birge jama'a.
Hotuna: Jerin kyawawan 'ya'ya 4 da shugaba Buhari ya aurar bayan hayewarsa mulki
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aurar da 'ya'yansa hudu tun bayan hayewarsa madafun iko a shekarar 2015.
Uku daga cikin bukukuwan an yi su ne cike da shagali, bidiri tare da aji irin na manya. Daya daga ciki ne kadai aka yi shi ba tare da wani gagarumin shagali ba.
Asali: Legit.ng