Sokoto: Kwastoma ya sharɓawa karuwa wuƙa bayan ta ƙi karbar N1,000 na 'aikinta'
- 'Yan sanda sun damke wani kwastoma wanda ya halaka 'yar magajiya har lahira bayan ya kwanta da ita a jihar Sokoto
- Kamar yadda aka gano, ya ba ta kudi N1000 ne matsayin hakkin 'aikin da tayi masa, amma ta raina tace ba za ta karba ba
- A cewarsa, ta dauko wuka tare da barazanar sharba masa, amma ya ci karfinta kuma ya kwace tare da sheke ta da ita
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto: Jami'an tsaro sun yi ram da wani mutum da ake zargi da halaka karuwa a karamar hukumar Dange/Shuni ta jihar Sokoto.
An tattaro cewa, kwastoman ya sharbawa karuwar wuka ne bayan fada ya kacame a tsakaninsu saboda ta ki karbar N1000 da ya bata bayan ya kwanta da ita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyi a yankin sun sanar da Punch cewa, karuwar tana zama ne a daya daga cikin gidajen karuwai dake yankin kuma sun yi kaurin suna wurin aikata ashsha.
Wata majiya tace makwabtan dake kusa da otal din da abun ya faru ne suka dinga kururuwa, lamarin da ya janyo hankulan jama'a masu wucewa har suka kama wanda ake zargin yayin da yayi yunkurin tserewa bayan ya gane cewa ta sheka lahira.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace wanda ake zargin yayi ikirarin cewa shi mai bincike ne wanda ya ziyarci jihar Sokoto domin yin binciken ilimi.
Abubakar yace wanda ake zargin ya yanke shawarar kwana a gidan yayan karuwar amma rikicin ya fara ne lokacin da ya biya ta N1000.
Kakakin rundunar 'yan sandan yace karuwar tace ba za ta karba kudin ba, wanda hakan yasa suka fara fada.
Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan yace, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa karuwar ta fito da wuka, wacce ya kwace tare da soka mata bayan ya ci karfinta.
Abubakar ya kara da cewa, an mika lamarin zuwa sashin binciken kisan kai na rundunar domin binciken da ya dace.
Yadda na kama mijina da 'dandazon' mata a gadon aurenmu, Matar Aure tayi bayani a bidiyo
A wani labari na daban, matar dake da muryar nan da 'yan kafar sada zumuntar zamani ke ta hawa wacce ke bayyana "dandazon mata cike da dakinta" ta bada labari a sabon bidiyo.
Idan za mu tuna, bidiyon ya yadu a cikin kwanakin nan inda take bayyana yadda mijin ta ya kwaso karuwai ya cika mata daki da su suna ta badala.
Duk da mutane sun ga cewa, matar tana bayanin ne a gaban kotu yayin da take korafi kan tsagwaron cin amana da neman mata irin na mijinta, sun dauka abun da nishadi.
Asali: Legit.ng