Buhari zai dawo da zaman lafiya a Najeriya kafin ya gama mulki a 2023, Malami

Buhari zai dawo da zaman lafiya a Najeriya kafin ya gama mulki a 2023, Malami

  • Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ya ce zaman lafiya zai dawo Najeriya kafin Buhari ya sauka
  • Ministan, wanda ya ta ya ɗaukacin al'ummar Musulmi murnar zuwan Babbar Sallah, ya ce Buhari na hana idon shi bacci domin cimma nasara
  • Ya ce ya na fatan Allah ya karbi add'o'in zaman lafiya da ɗorewar kwanciyar hankali a jihar Kebbi da Najeriya baki ɗaya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Ministan shari'a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya ce kafin karewar wa'adin gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari shekara mai zuwa, ɗaukakar Najeriya zata dawo, zaman lafiya zai samu gindin zama.

Malami ya ce shugaba Buhari na aiki tuƙuru da hana idonsa bacci domin tabbatar da komai ya koma kan hanya, ba miƙa mulki cikin ruwan sanyi ba kaɗai, har da tabbatar wa ƙalubalen tsaron da ya addabi ƙasa ya zama tarihi.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Ministan Shari'a, AGF Abubakar Malami.
Buhari zai dawo da zaman lafiya a Najeriya kafin ya gama mulki a 2023, Malami Hoto: Inside Bauchi State/facebook
Asali: Facebook

Ministan ya yi wannan furucin ne yayin da yake ta ya ɗaukacin al'ummar Musulmi murnar zagayowar babbar Sallah (Eid-El-Adha) ta wannan shekarar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Malami na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina son sake tabbatar muku da cewa gwamnatin shugaban ƙasa Buhari ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen cigaba da yin duk me yuwuwa ta dawo da ingantaccen tsaro a faɗin ƙasa."

"Ina fatan Allah SWT zai amsa dukkan Addu'o'in mu na samun zaman lafiya mai ɗore wa a jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya, haka nan kuma da miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi a farkom shekara mai kama wa."

Ba zan huta ba sai yan Najeriya sun samu sassaucin rayuwa - Buhari

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ba zai taɓa haɗa layi da hutu ba har sai yan Najeriya sun samu zaman lafiya

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Ganduje ya faɗi wanda Bola Tinubu ya amince zai zaɓa a matsayin mataimaki na gaske

Shugaban ya sake tabbatar wa yan Najeriya cewa ba zai huta ba har sai sun samu nutsuwa daga gare shi duba da kalubalen tsaro da tsadar rayuwa da suka dabaibaye ƙasar nan.

Yayin taya Musulmai murnar zuwan Sallah, Buhari ya ce da kowa na koyi da koyarwan addini da duk matsalolin nan sun zama tarihi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262