Kyawawan Hotunan Buhari da Yusuf a Filin Sallar Idin Babbar Sallah Sun Kayatar
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallaci idin babbar sallah a masallacin idi na Kofar arewa dake garin Daura a jihar Katsina
- Ba shugaban kasan kadai aka gani ba, ya garzaya masallacin tare da 'dan shi namiji daya tilo, Yusuf Muhammadu Buhari
- A kyawawan hotunan sallar idin da suka bayyana, an ga Talban Dauran da mahaifinsa suna sallah kafada da kafada
Daura, Katsina - Shugaban kasa Muhanmadu Buharui ya garzaya garinsu, Daura dake jiha Katsna tun ranar Juma'a domin yin hutun babbar sallah a can.
A ranar Asabar, 9 ga watan Yulin 2022 ne aka yi babbar sallah wacce take daidai da rana 10 ga watan Dhul Hijja. Musulmai daga dukkan fadin duniya sun sallaci sallar idin babbar sallah
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ma ba a bar shi a baya ba tunda ya garzaya masallacin Kofar Arewa tare da 'yan uwa Musulmi inda yayi sallarsa ta Idi.
A kyawawan hotunan da suka bayyana, shugaban kasan ya je Masallacin Idin tare da 'dan shi namiji daya tilo, wato Yusuf Muhammadu Buhari, wanda a kwanakin baya aka bashi sarautar Talban Daura a masarautar daura mai tsohon tarihi.
Ga kyawawan hotunansu:
AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana
A wani labari na daban, a ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Muhammadu Buhari da AGF Abubakar Malami, SAN.
An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.
Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan. "Eh, da gaske ne, antoni janar na tarayya ya aura diyar shugaban kasa."
Asali: Legit.ng