Rashin tsaro zai ragu idan ‘yan Najeriya suka fara mutunta addinan juna
- limamin babban masallacin Calabar ya ce Rashin tsaro zai ragu idan ‘yan Najeriya suka fara mutunta addinan juna
- Alhaji Olowolayemo yace babban matsalar dake fuskanta yan Najeriya shine son kai da rashi la'akari da yadda wasu keji
- Limamin yayi kira da daukacin al'umman musulmi da koyi da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) don samun dawwamammen zaman lafiya
Jihar Cross Rivers - Babban limamin babban masallacin Calabar, Alhaji Kabir Olowolayemo, ya ce za a iya dakile matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Najeriya idan ‘yan kasar suka mutunta addinin juna kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta rawaito.
Alhaji Kabir Olowolayemo ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Calabar ranar Asabar da ake bikin Eid-El-Kabir.
Ya ce Sallah ita ce sadaukarwar da kai da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna a lokacin da yake raye, ya kuma bukaci kowa da kowa ya yi koyi da shi don samun dawwamammen zaman lafiya.
“Babban matsalar da muke da ita a Najeriya ita ce son kai mun damu da kanmu ne kawai ba tare da la’akari da yadda wasu ke ji ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Shawarata ga daukacin al’ummar kasar nan ita ce, idan har muna son ganin an magance matsalar rashin tsaro da rashin zaman lafiya, to mu mutunta juna ba tare da la’akari da addini da kabilanci ba,” inji shi.
Ya ce ya kamata addini ya taka muhimmiyar rawa wajen sasanta ‘yan kasa, ba raba kan YAN kasar ba.
Mista Olowolayemo ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su bari addini da ra’ayin kabilanci ya lullube tunaninsu ga aikin gina kasa.
“Najeriya kasa ce na sakulanci kada mu yi amfani da addini ko kabila a matsayin ma’auni wajen zabar shugabanninmu, ya kamata mutane su yi zabe bisa cancanta.
"Dole ne mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu kuma mu je mune mu ingantattun yan takara wanda za su iya kawo mafita ga dimbin kalubalen da muke fuskanta a kasar," in ji shi.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya daga kasar Faransa. Rahoton jaridar PUNCH
Tinubu ya bayyana haka a shafin na sa Tuwita, da Instagram a cikin jirgin sama ya rubuta “ hanyar zuwa gida”.
Asali: Legit.ng