Arzikin nufin Allah: Kudi sun karu, Dangote ya zama na 65 a jerin masu kudin duniya
- Attajirin nan da ya fi kowa kudi a Afirka Aliko Dangote a cikin watanni shida da suka gabata ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya
- Idan aka kwatanta da mafi yawan hamshakan attajirai, tun farkon yakin Ukraine da yawa arzikinsu raguwa yake
- Zuckerberg, wanda ya ga kasa-kasa a dukiyarsa a ’yan watannin nan, yanzu ya koma bayan wata mata da aka ce ita ce mafi arziki cikin matan duniya
Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya na Bloomberg, daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, a cewar Bloomberg, yana da dala biliyan 20.4 kamar yadda a ranar Juma'a 8 ga Yuli, 2022, kuma hakan ne ya kai shi ga matsayi na 65 a mafi arziki a duniya.
Rahoton ya kuma nuna cewa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yuli, Dangote ya samu dala biliyan 1.30, wanda hakan ya taimaka masa wajen barin matsayi na 100 da yake a farkon 2022.
Shi dai wannan jadawali na jeri ne na shekara-shekara wanda ke ba da hoto na dukiyar attajirai ta amfani da farashin hannun jari da farashin musaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Akwai sama da hamshakan attajirai 500 da aka gano a cikin jerin wadanda suka hada da Dangote, kuma shi kadai ne dan Najeriya.
Mace ta banke Zuckerberg a jerin attajirai
A halin da ake ciki dai, dukiyar mace mafi arziki a duniya, Francoise Meyer, ta zarce na shugaban kamfanin Meta (uwa ga Facebook, Instagram, WhatsApp dss), Mark Zuckerberg.
A ranar Laraba, 6 ga Yuli, kamfanin danginta, L'Oreal, ya sharbi ribar 4.92% a karshen cinikin kasuwar Turai a ranar.
Hakan ya taimaka mata wajen tattara Naira Tiriliyan 1.3 (dala biliyan 3.1), inda ta kai ga mallakar dalar Amurka biliyan 71.6 tare da sanya ta a matsayi na 14 mafi arziki a duniya.
A daya bangaren kuma Zuckerberg yana da darajar dukiya dala biliyan 61.1, inda ya fadi kasa da Meyers a matsayi na 17 bayan da ya kai matsayi na 6 a farkon shekarar nan.
Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci
A wani labarin, idan aka hada dukiyar Alhaji Aliko Dangote da na Mike Adenuga, su biyun kawai sun fi mutane miliyan 63 da ke Najeriya yawan arzikin kudi.
Wani rahoto da ya fito daga Oxfam, ya nuna Attajiran da ake ji da su, sun fi daya bisa ukun ‘yan Najeriya arziki, idan za a tattara duk abin da suka tara.
Aliko Dangote shi ne shugaban kamfanin Dangote Group, Mike Adenuga ne wanda ya mallaki kamfanin sadarwa na Globacom da ya yi fice a Najeriya.
Asali: Legit.ng