Da duminsa: An nemi fitaccen mai garkuwa da mutane, dillalin makamai an rasa a kurkukun Kuje

Da duminsa: An nemi fitaccen mai garkuwa da mutane, dillalin makamai an rasa a kurkukun Kuje

  • Majiyoyi daga jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, fitaccen mai garkuwa da mutane kuma dillalin makamai ya tsere daga magarkamar Kuje
  • Hamisu Wadume, 'dan asalin jihar Taraba, baya daga cikin masu laifin da aka sake cafkewa ko suka dawo da kansu gidan yarin
  • Wadume 'dan ta'adda ne da ya addabi jihar Taraba kuma yayi sanadin mutuwar jami'an IRT 3 karkashin Abba Kyari

Abuja - Majiyoyin tsaro a Abuja sun bayyana cewa, fitaccen mai garkuwa da mutane kuma dillalin makamai 'dan asalin jihar Taraba, Hamisu Wadume wanda aka kama tare da garkamewa sakamakon hannu a kisan jami'an IRT 3, yana daga cikin mazauna gidan yarin kuje da suka cikawa bujensu iska a farmakin daren Talata da 'yan ta'adda suka kai gidan gyara hali na Kuje.

An tattaro cewa, Wadume wanda ke garkame a gidan yarin Kuje tun 2020, ya yi batan-dabo kuma bashi daga cikin wadanda aka sake kamawa ko kuma suka dawo da kansu bayan farmakin da 'yan ta'addan suka kai, jaridar Vanguard ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Tawagar shugaban kasa basu tabuka komai ba a lokacin da yan bindiga suka auka masu – Mazauna kauyukan Katsina

Haruna Wadume
Da duminsa: An nemi fitaccen mai garkuwa da mutane, dillalin makama an rasa a kurkukun Kuje. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Jami'an rundunar IRT ne suka kama Wadume a Takum, jihar Taraba sakamakon addabar jama'ar jihar da yayi da ta'addancinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma jami'an rundunar IRT sun fuskanci ruwan wuta daga sojojin bataliya fa 93 dake Takum a jihar Taraba inda suka halaka 'yan sanda uku da ma'aikaci daya farar hula kan cewa ba su bayyana ko su waye su ba kuma abun hawansu bai bayyana su 'yan sanda bane.

Sojojin da suka ceci Wadume daga hannun jami'an IRT an gano cewa sun yi wannan aika-aikar ne bisa umarnin kwamandansu.

Bayan cetonsa da sojojin suka yi, ya tsere tare da boyewa a jihar Taraba.

Daga bisani, jami'an IRT sun sake cafke shi a Kano kuma suka kai shi Abuja inda aka mika shi gaban kotu wanda hakan ya kai shi gidan yarin Kuje.

Harin kurkukun Kuje: Ido rufe 'yan ta'adda suka dinga neman inda Abba Kyari yake

Kara karanta wannan

Kyari, Maina, tsofaffin Gwamnoni da jerin wadanda ke tsare a gidan yarin Kuje

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kai farmaki gami da kubutar da sama da 'yan gidan yarin Kuje 600 a daren Talata, tare da neman inda DCP Abba Kyari yake amma basu samu nasarar fasa bangon bangaren gidan yarin da yake tsare ba.

Wata majiyar sirri ta bayyana yadda bayan tabbatar da an saki 'yan Boko Haram 64, tawagar 'yan ta'addan suka bazama bincikar daki-dakin wadanda suka zabi zama tare da tambayar inda Abba Kyari yake, ina Abba Kyari?

Yayin da suka samu labarin inda hazikin jami'in tsaron yake, sun garzaya wajen amma a rashin sanin su, an kara masa tsaro na musamman gami da canza masa daki kusa da kofar shiga wanda 'yan ta'addan ba zasu iya shiga ba, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng