Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun babbar Sallah

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun babbar Sallah

  • Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata, 11 da 12 ga watan Yuli, 2022 a matsayin na hutun shagalim babbar Sallah
  • Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya taya ɗaukacin Musulman Najeriya murnar zagayowar wannan rana
  • Ya bukaci kowa ya ɗauki nauyin kai rahoton duk wani ko ayyukan laifi da basu yarda da su ba a kewayen su

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 11 ga watan Yuli, da Talata 12 ga watan Yuli, 2022 a matsayin ranakun hutun babbar Sallah (Eid-el-Kabir).

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana ranakun hutun a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da Sakataren dindindin na ma'aikatar, Dakta Shuaib Belgore, ya fitar ranar Alhamis.

Rauf Aregbesola.
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun babbar Sallah Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Ya ta ya ɗaukacin al'ummar Musulmai da yan Najeriya na cikin gida da waɗan da ke zaune a ƙasashen waje murnar zuwan Babbar Sallah, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin jiha ta rushe cocin wani fitaccen faston da ake kai ruwa rana dashi

Ministan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina kira ga yan uwa Musulmai da su cigaba da nuna soyayya, zaman lafiya, kyawawan halaye da sadaukarwa kamar yadda suka koya daga halayen Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW)."
"Haka nan kuma su yi amfani da wannan lokacin su roki Allah zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da kuma tsayuwar ƙasar nan duba da ƙalubalen tsaron da muke fama da shi a yanzu."

FG zata tsare yan Najeriya da dukiyoyin su - Minista

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, "ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tsare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya, tallafa musu, ayyukan jin kai, da samar da tsaro a makarantu."

Aregbesola, yayin da yake taya Musulmai murna, ya roke su da su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani basu yarda da shi ba a kewayen su ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Kotun Birtaniya ta umarci a tsare Sanata Ekweremadu da matarsa, ta yanke hukunci kan shekarun mai ba da Ƙoda

Ya roki su yi amfani da manhajar N-Alert da aka ƙirkira don kai rahoton wani abu da zummar shawo kan yaɗuwar ƙalubalen tsaro, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Kotun Birtaniya ta umarci a tsare Sanata Ekweremadu da matarsa, ta yanke hukunci kan shekarun mai ba da Ƙoda

A yau Alhamis, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa sun gurfana a gaban Kotun Majistire ta ƙasar Birtaniya kan zargin yanke sassan jiki.

Bayan tafka muhawarawa tsakanin ɓangarori biyu, Kotu ta yanke cewa wanda ake shari'ar kansa, shekarunsa 21 ba 15 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262